Tirkashi: Dan El-Rufai ya yi wa Buhari barazana kan nadin sabbin ministoci

Tirkashi: Dan El-Rufai ya yi wa Buhari barazana kan nadin sabbin ministoci

Bello, dan gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana damuwarsa kan nade-naden da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na 'yan fadarsa inda ya yi barazanar yin zanga-zanga idan Buhari ya sake nada tsaffin ministocinsa karo na biyu.

Bello El-Rufai ya ce 'yan Najeriya za su juya wa Buhari baya muddin ya sake ministocin da ya yi aiki da su a zangon mulkinsa na farko.

A rubutun da ya wallafa a shafinsa na Twitter a daren Juma'a, Bello ya ce, "Mun yarda da kai shugaban kasa. Wannan ba zancen bangaranci bane kuma ba ta da alaka da irin kaunar da al'umma ke maka da kowa ya sani. Amma idan ka sake dawo da wasu tsaffin ministocinka. Nagartar da ke ke da ita za ta ragu. Za ka ji daga gare mu. Mu ba 'yan PDP bane."

DUBA WANNAN: Kannywood: Adam Zango ya nuna sabuwar babbar mota ta miliyan N23m da ya saya

A dai jiya ne Shugaba Buhari ya sake nada Boss Mustapha a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya da kuma Abba Kyari a matsayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa duk da cewa wasu na tsamanin da zai sake nada su ba.

Sanarwar da ta fito daga bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya ce dukkan nade-naden za su fara aiki daga ranar 29 ga watan Mayun 2019.

Kazalika, 'Yan Najeriya da dama da jam'iyyun adawa da masana tattalin arziki da masu saka hannun jari na kasashen waje sun bayyana damuwarsu kan jinkirin da shugaban kasar ke yi wurin nada sabbin ministocinsa.

Idan aka yi la'akari da sanarwar da ta fito daga fadar shugaban kasa, akwai alamun shugaban kasar ya fi bayar da fifiko ne wurin nada hadimansa na kut da kut.

Galibin sunayen hadimai 11 da shugaban kasar ya nada mutane ne daga arewcin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel