An haramta sanya Niqabi a kasar Tunisya

An haramta sanya Niqabi a kasar Tunisya

- Hare-haren kunar bakin waken ya tilastawa kasar Tunisiya hana sanya kwalliyan Musulunci

- Tufafin Niqabi wata yar kyalle ne da mata ke sanyawa na rufe fuskarsu domin rage fitina cikin al'umma

- Gwamnatin kasar na tsoron wasu zasu iya amfani da wannan tufafi wajen yin aika-aika

Firam ministan kasar Tunisiya. Youssef Chahed, ya haramtawa matan kasarsa sanya kwalliyar Musulunci ta Niqabi saboda dalilai na tsaro.

Majiya mai karfi ya bayyanawa Reuters ranar Juma'a cewa: "Chahed ya rattaba hannu da dokar hana mutane masu rufe da fuskokinsu shiga wani ginin gwamnati, ma'aikatu, da makarantu domin dalilai na tsari,"

Wannan shawara ya biyo bayan tsananta al'amarin tsaro a kasar Larabawa inda yan ta'adda suka kai harin kunar bakin wake sau biyu ranar 27 ga watan Yuni inda mutane biyu suka rasa rayukansu kuma bakwai suka jikkata.

KU KARANTA: Kotun zaben shugaban kasa: Atiku ya gabatar da hujjoji 26,000 don tabbatar rinto akayi masa

Idanuwan shaida sun laburta cewa daya daga cikin yan kunar bakin waken na sanye da Niqabi, amma ma'aikatar harkokin cikin gida ta musanta haka inda tace kawai dan kunar bakin waken ya tayar da Bam din ne yayin tserewa jami'an hukumar

Wannan hari shine na uku da aka kai cikin mako daya, a lokaci da kasar ke karban baki kuma ana shirye-shiryen zaben majalisar dokokin kasar.

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin wadannan hare-hare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel