Kotun zaben shugaban kasa: Atiku ya gabatar da hujjoji 26,000 don tabbatar rinto akayi masa

Kotun zaben shugaban kasa: Atiku ya gabatar da hujjoji 26,000 don tabbatar rinto akayi masa

Dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin lemar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), da jam'iyyarsa sun gabatar da hujjoji 26,175 kan zaben shugaba Muhammadu Buhari a kotun zaben shugaban kasa dake Abuja.

Lauyan Atiku, Livy Uzoukwu, ya fara gabatar da hujjoji 5,196 ranar Alhamis, kafin ya gabatar da sauran ranar Juma'a.

Atiku yana kulabalantar nasarar da shugaba Muhammadu Buhari ya samu inda yace kuri'un da ya samu ya fi na shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) yawa.

Mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya ce hujjojin sune takardun sakamakon zabe daga akwatunan zabe na kananan hukumomi a jihohi takwas na Katsina, Kebbi, Borno, Jigawa, Gombe, Bauchi, Kaduna da wani sashen Kano.

KU KARANTA: Dalilin da ya sanya nike zagaye a Kwara – Gwamna Abdulrazak

Ibe ya lissafa takardun kamar haka; 3,378 daga jihar Katsina; 2,106 daga jihar Kebbi; 3,472 daga jihar Borno; 3,162 daga Jigawa; 1,912 daga Gombe; 3,539 daga Bauchi; 3,335 daga Kaduna da 5,271 daga jihar Kano.

Lauyan INEC, Yunus Usman; Mike Igbokwe, lauyan Buhari da Charles Edosomwan, lauyan APC, sun nuna rashin yardarsu da takardun da PDP ta gabatar.

Amma sun bayyanawa kotun cewa zasu bayyana dalilin rashin yardarsu idan PDP ta kammala gabatar da shaidunta.

An dakatad da karar zuwa ranar Litinin, 8 ga wtaan Yuli domin cigaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel