Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin kwace kadarori 14 mallakar wani sanata

Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin kwace kadarori 14 mallakar wani sanata

Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta bawa gwamnati umurnin kwace wasu kadarori mallakar Sanata Peter Nwaoboshi na tsawon wani lokaci.

Kotun ta fara bayar da umurnin kwace kadororin sanatan 14 da asusun ajiyar kudade na banki 22 na Mista Nwaoboshi ne tun a ranar Talata.

An bayar da umurnin karbe asunsun ajiyar da ke bankunan Zenith, Access, Sterling da UBA cikin takardar da kotu ta bayar kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

An bawa sanatan mai wakiltan mazabar Delta Ta Arewa wa'addin kwanaki 30 ya bayyana wa kotu yadda ya samu kadarorin idan kuma ba haka gwamnati za ta rike kadarorin ta antaya su zuwa baitil mali.

DUBA WANNAN: Kannywood: Adam Zango ya nuna sabuwar babbar mota ta miliyan N23m da ya saya

Hakan na zuwa ne bayan an zurfafa bincike kan kadarori da kudade da Mista Nwaoboshi ya mallaka wanda gwamnatin tarayya ke zargin cewa ta hanyar haramun ya same su.

A baya, an taba gurfanar da sanatan a gaban kotu inda aka tuhume shi da laifin rashin bayyana dukkan kadarorinsa kamar yadda doka ta tanada amma kotun da ke da hurumin sauraron karar a Abuja tayi watsi da karar a dalilin rashin bin ka'ida wurin shigar da karar.

A halin yanzu, Mista Nwaoboshi yana fafatawa a kotu da wani lauya mazaunin Abuja, Ned Nwoko kan nasarar takarar lashe zaben kujerar sanata na mazabar Delta Ta Arewa duk da cewa an ambata Nwaoboshi a matsayin wanda ya lashe zaben na Fabrairun 2019.

Kotun koli ta bayar da umurnin gaggauta zartar da hukunci kan karar da Nwoko ya shigar na kallubalantar nasarar Nwaoboshi kuma an sa ran kotu za ta bayar da hukuncin ta nan da 'yan kwanaki kadan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel