Fashewar na'urar lantarki ya tilastawa jirgin sama saukan dauke da fasinjoji 217 saukan gaggawa

Fashewar na'urar lantarki ya tilastawa jirgin sama saukan dauke da fasinjoji 217 saukan gaggawa

Wani jirgin kamfanin Virrgin Atlantic ya yi saukar gaggawa a birnin Boston bayan wuta ta kama a cikin jirgin sakamakon fashewa da na'urar cajin wayan tarho 'power bank' ya yi a cikin jirgin.

BBC ta ruwaito cewa jirgin ya taso ne daga New York yana kan hanyarsa na zuwa Landan a daren Alhamis lokacin da wutar ta kama wadda hakan ya tilastawa jirgin sauka ba shiri.

An kwashe dukkan fasinjoji 217 da ke cikin jirgin a filin tashi da saukan jirage na Boston Logan kuma babu wanda ya yi wani rauni mai tsanani.

DUBA WANNAN: Yanzu Yanzu: Tsohon ministan PDP da dan sa sun karbi katin zama 'yan APC

'Yan sanda suna kyautata zaton power bank na cajin wayan tarho ne ya janye gobarar.

Jami'an tsaro masu kashe bam sun bincika cikin jirgin bayan ya sauka kuma sun gano na'urar a tsakanin kujerun jirgin inda wutar ta fara ci.

"Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa na'urar tayi kama da na'urar cajin waya," a cewar mai magana da yawun 'yan sandan.

Sai dai daya daga cikin fasinjojin jirgin, Maria ta musanta hakan inda ta shaidawa majiyar Legit.ng cewa tana hira da abokinta lokacin da kujerarsa ta kama da wuta.

Ta ce bata amince da rahoton da aka fitar na cewa na'uarar cajin waya ce ta janyo gobarar ba.

"Cikin mintuna biyu aka kashe wutar," inji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel