Ruga: Dattijan Arewa sun nemi ayi dokar hana musgunawa makiyaya

Ruga: Dattijan Arewa sun nemi ayi dokar hana musgunawa makiyaya

Kungiyar Dattawa Arewa (NEF) ta shawarci gwamnatin tarayya da na jihohi su fito tsare-tsare da za su kare yadda ake cin zarafin Fulani da shanunsu a kasar nan.

Mataimakin shugaban kungiyar, Ambasada Yahaya Kwande ya bukaci gwamnonin jihohin Arewa da sauran masu fada a ji da su dauki mataki kan batun cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a a Abuja.

Kungiyar ta ce ya zama dole dukkan masu ruwa da tsaki a kasar nan suyi taka tsantsan domin kare asarar rayuwa da dukiyoyi ta hanyar kaucewa aikata wani abu da zai janyo tashin hankali tsakanin 'yan Najeriya.

DUBA WANNAN: Kannywood: Adam Zango ya nuna sabuwar babbar mota ta miliyan N23m da ya saya

Ta ce za ta gana da gwamnonin jihohin Arewa kan batun da jingine tsarin samar da rugar kiwo na makiyaya da gwamnatin tarayya ta yi.

"Ya zama dole gwamnatin tarayya da na jihohi su bullo da tsare-tsaren da zai kare cin mutuncin da ake yi wa Fulani da shanunsu da kuma kwantar da tarzomar da ka iya tasowa da zai janyo asarar dabobi da rashin zaman lafiya a kasar.

"Kungiyar tana lura da rikicin da ya barke sakamakon zartar da shirin samar da rugar da gwamnatin tarayya tayi da kuma irin matakin da gwamnatocin jihohin Kudu da wasu wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka dauka kan lamarin."

NEF ta ce kungiyoyi da dama sun tuntube ta domin neman ta yi amfani da matsayar ta wurin kwantar da hankulan mutane tare da taimakawa wurin warware matsalar da yi wa kowa adalci.

Ta kuma ce za ta gana da shugaban kungiyan gwamnonin Arewa, Simon Bako Lalong a mako mai zuwa domin tattaunawa kan hanyoyin da za a magance matsalar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel