Kotun koli: Lokaci ya yi da mutanen Jihar Osun za su mori Gwamnatin APC Inji Tinubu

Kotun koli: Lokaci ya yi da mutanen Jihar Osun za su mori Gwamnatin APC Inji Tinubu

Babban jagoran jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, ya yaba da hukuncin da kotun koli ta dauka a game da zaben jihar Osun inda ta tabbatar cewa APC ce ta lashe zaben na 2018.

A wani jawabi da Bola Tinubu ya fitar a Ranar Juma’a 5 ga Watan Yuli, 2019, bayan ta tabbata gwamna Isiaka Adegboyega Oyetola ya samu nasara, ya ji dadin abin da Alkalan kasar su ka yi.

Tinubu ya ce wannan shari’a ya nuna cewa kotu ta na aiki wajen tabbatarwa jama’a zabin su. “Duk da barazana da karyayyaki da kage iri-iri, kotun koli ta yi hukunci ba tare da son-kai da jin tsoro ba.”

Jagoran na APC ya taya gwamna Gboyega Oyetola murna inda ya yi kira a gare sa ya yi aiki da kowa. Tinubu ya na mai cewa Alkalai sun yi amfani da karfin hujja ne ba surutun jama'a ba.

Tinubu ya ce: “Ina mai taya gwamna Oyetola murnar tsaya tsayin-daka da ya yi a lokacin wannan shari’a. Ina kuma jinjinawa gwamnati da mutanen jihar Osun da su ka bi doka yayin da kotu ta ke aikin ta.

KU KARANTA: Buhari ya taya gwamnan Osun murnar samun nasara a kotun koli

A game da batun kudirin zabe, Tinubu, ya bayyana cewa hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta watau INEC ce kutum ke da hurumin amfani da doka a yadda ya dace, kuma ta yi abin kirki a zaben Osun.

Tsohon gwamnan ya kuma kara da cewa: “A yanzu za a fara aiki gadan-gadan a jihar Osun domin jama’a su girbi shukar da su ka yi, bayan babban kotun kasar ta rusa duk wata sarkakiyar shari’a”

A jawabin na sa, Bola Tinubu ya ji dadin yadda APC ta tsaya bayan gwamnan na ta, sannan ya yabawa yadda PDP da ‘dan takararta, Sanata Ademola Adeleke, kan yadda su ka nemi hakkin su a kotu.

“Lokaci ya yi da jama’a za su hada-kai su hada hannu da gwamnatin jihar wajen ciyar da Osun zuwa mataki na gaba.” Inji Tinubu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel