Talauci: Magidanci ya yanka 'ya'yansa biyu, ya kashe mahaifiyarsu saboda ta yi 'ihu'

Talauci: Magidanci ya yanka 'ya'yansa biyu, ya kashe mahaifiyarsu saboda ta yi 'ihu'

An kama wani magidanci, mai shekaru 35, ranar Alhamis bayan ya kashe 'ya'yansa tare da fille kan matarsa a gundumar Talensi da ke kasar Ghana.

Magidancin, mai suna Collins Yagbil, ya dauki dan sa namiji da diyarsa mace zuwa wata tsangayar tsatsiba domin sadaukar da su ga abin bautarsu.

Yagbil ya yi wa dan sa namiji yankan Rago a cikin tsangayar. Hakan ne ya saka diyarsa Mace ta fara kuka, lamarin da ya fusata Yagbil, wanda nan take ya kama yarinyar tare da datse mata hannaye kafin daga bisani ita ma ya yi mata yankan rago.

Magidancin ya debi jinin 'ya'yan na sa tare da watsa shi a jikin wani dutse.

Matar Yagbil ta garzayo zuwa wurin bayan ta fahimci cewa wani na faruwa, kuma da isowar ta wurin ta iske gawar yaran, a kwance malemale cikin jini, a kan dutse. Nan ta ke ta kurma ihun neman taimako domin jawo hankalin jama'a.

DUBA WANNAN: Magidanci ya kwankwadi 'sniper' bayan ya kama matarsa turmi da tabarya da tsohon saurayin ta

Amma a kokarinsa na rufe mata baki, Yagbil ya far wa matar tare da datse mata kai. Lamarin ya fusata 'yan uwan matar, wadanda suka umarci jama'a da su kashe Yagbil, amma daga baya sai suka mika shi hannun 'yan sanda.

Da su ke magana da manema labarai, dangin matar sun bayyana cewa Yagbil ya fara wasu irin dabi'u a wasu lokuta da suka wuce amma sai suka dauka ko shaidanu ne suka shiga jikinsa. Kazaliak, sun bayyana cewa yanzu sun fahimci cewa ya samu tabin hankali ne bayan ya kashe matarsa da 'ya'yansu biyu.

Ana cigaba da bincike a kan lamarin domin gano ainihin dalilin da ya saka Yagbil ya sadaukar da 'ya'yansa. Sai dai wasu na gani talauci ne ya saka aikata hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel