Da duminsa: Buhari zai hallarci taron AU a Nijar ranar Asabar

Da duminsa: Buhari zai hallarci taron AU a Nijar ranar Asabar

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai bar Abuja zuwa birnin Niamey da ke Jamhuriyar Nijar a ranar Asabar 6 ga watan Yuli domin hallartar taron Kungiyar Hadin Kan kasashen Afirka (AU) da za a gudanar a ranar 7 ga watan Yuli.

Sanarwar da hadimin shugaban kasa kan kafafen yada labarai, Femi Adesina ya fitar ya ce Buhari zai hallarci taron kungiyar karo na 12 inda za a tattauna kan batun yarjejeniyar kasuwanci na kasashen Afirka (AfCFTA).

Ana sa ran shugabanin kasashen na Afirka za su kaddamar da shirin kasuwancin na AfCFTA da zai sawaka kasuwanci tsakanin kasashen na Afirka.

DUBA WANNAN: Kannywood: Adam Zango ya nuna sabuwar babbar mota ta miliyan N23m da ya saya

Kafin taron, Shugaba Buhari ya tattauna da masu ruwa da tsaki da masana kasuwanci har ma da kwamiti da ya kafa kan batun kafin Najeriya ta amince da saka hannu kan yarjejeniyar kasuwancin.

"Kwamitin da Shugaban kasa ya kafa ta shawarci shugaban Najeriyan ya sanya hannu kan yarjejeniyar saboda za ta inganta kasuwanci tsakanin kasashen Afirka.

"Shugaba Buhari zai saka hannu kan yarjejeniyar ta AfCFTA a wurin taron na AU a Niamey," a cewar Adesina.

Shugaba Buhari zai tafi wurin taron ne tare da First Lady, Misis Aisha Buhari; Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, Gwamna Atiku Bagudu na Kebbi da Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina.

Ana sa ran shugaban kasar zai dawo Abuja bayan kammala taron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel