Yanzu-yanzu: Buhari ya alanta nadin hadiman kut da kut 11

Yanzu-yanzu: Buhari ya alanta nadin hadiman kut da kut 11

Bayan dade da jiran tsammani, shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da nadin wasu ma'aikatan cikin gidan gwamnati na kusa da shi a ranar Juma'a, 5 ga watan Yuli, 2019.

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya bayyana hakan ne da yammacin nan a shafin ra'ayi da sada zumuntarsa.

Yace: "Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da nadin hadiminsa na kut da kut

1. Mohammed Sarki Abba – Babban Hadimin shugaban kasa kan bukukuwa da harkokin gida

2. Ya’u Shehu Darazo – Babban hadimin shugaban kasa kan harkokin na musamman

3. Dr Suhayb Sanusi Rafindadi – Likitian shugaban kasa na musamman

4. Amb. Lawal A. Kazaure – Shugaban Frotokol

5. Sabiu Yusuf – Hadimin ofishin shugaban kasa

6. Saley Yuguda – Hadimin shugaban kasa kan gyaran gida

7. Ahmed Muhammed Mayo – Hadimin shugaban kasa kan harkokin kudi

8. Mohammed Hamisu Sani – Hadimi kan harkoki na musamman

9. Friday Bethel – Hadimin kut da kut na harkoki

10. Sunday Aghaeze – Mai daukan hoton kasa

11. Bayo Omoboriowo – Mai daukan hoton shugaban kasa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel