Siyasa: Prince Apugo ya yi kira mutanen Ibo su rungumi Jam’iyyar APC

Siyasa: Prince Apugo ya yi kira mutanen Ibo su rungumi Jam’iyyar APC

Babban jigon jam’iyyar APC a Kudancin Najeriya, Prince B.B. Apugo, ya nemi mutanen Kudu maso Gabashin Najeriya su yi maza su koma jam’iyyar APC mai mulki domin a dama da su a siyasa.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust, Prince Apugo, ya bayyana cewa idan har mutanen Ibo na da niyyar karbar shugabanci a 2023, dole su bi jirgin jam’iyyar APC a yanzu.

Prince Apugo ya yi wannan bayani ne a wata hira da ya yi kwanan nan a Abuja inda ya ce dole mutanen Ibo su marawa shugaba Muhammadu Buhari baya domin su samu makaman gwamnati.

Sai dai Jagoran na APC ya na ganin bai kamata tun yanzu a fara hasashen wanda zai karbi shugabancin kasar nan a 2023 ba. Apugo ya ce a kan batun 2023; “Wannan wani dogon hange ne!”

A kan batun ko Ibo zai iya zama shugaban kasa, Apugo ya ke cewa: “Yin hasashe bai laifi bane, amma a gani na, ya yi wuri sosai a soma maganar 2023 a lokacin da ba mu gama da 2019 ba.”

KU KARANTA: PDP ta dakatar da wasu 'Yan Majalisar Tarayya 7 daga Jam'iyya

Jagoran jam’iyyar mai mulki ya kara da cewa:

"Sai an kafa gwamnati, an samu Ministoci a kasa, zuwa shekarar 2020, 2021, sai a fara maganar zaben 2023. Babu wanda ya san wa zai kai lokacin a raye." Apugo ya ce: "Mutum ba Ubangiji bane!”

Babban ‘Dan siyasar ya kuma bayyana cewa akwai bukatar gwamnonin Kudu maso Gabas su ajiye siyasar adawa a gefe guda, su sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC saboda su kurbi romon mulki.

Jagoran na APC ya kuma jara da cewa jihar Ebonyi ce kurum ta iya ba shugaba Buhari 25% na kuri’un ta a zaben 2019. Apugo ya ce APC ta gaza samun wannan a Imo, Anambra, Abia da Enugu.

A karshe tsohon ‘dan jam’iyyar ta PDP ya bayyana cewa bai ji dadin ganin yadda manyan ‘yan siyasa irin su Rabiu Kwankwaso, Bukola Saraki da Yakubu Dogara su ka sauya-sheka a bara ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel