PDP ta dakatar da mambobin ta 7 a majalisar wakilai

PDP ta dakatar da mambobin ta 7 a majalisar wakilai

Kwamitin gudanar wa (NWC) na jam'iyyar PDP ya sanar da dakatar da Honarabul Ndudi Elumelu da sauran wasu mambobin ta shida a majalisar wakila.

Ragowar mambobin shida su ne; Honarabul Wole Oke, Honarabul Lynda Ikpeazu, Honarabul Anayo Edwin, Honarabul Gideon Gwadi, Honarabul Toby Okechukwu da Honarabul Adekoya Abdulmajid.

A ranar Alhamis ne NWC ya gayyace su domin amsa tuhumarsu da aikata laifukan haddasa rikicin shugabanci a tsakanin mambobin jam'iyyar a zauren majalisar wakilai ranar Laraba.

A cewar NWC, laifin da mambobin suka aikata daidai ya ke da yi wa jam'iyya rashin biyayya, a saboda an dakatar da su na tsawon wata guda.

A nata bangaren, majaliar wakilai ta bayyana cewa ta kafa wani kwamitin wucin gadi da zai biciki rikicin da ya faru a zauren majalisar a kan bayar da mukamin shugaban marasa rinjaye.

DUBA WANNAN: Gawa ta ki rami: Matashi Mohammed ya mike zumbur bayan an haka kabarun binne shi

An samu hatsaniya a zauren majalisar ne bayan shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila, ya yi gaban kan shi wajen bayyana sunan Ndudi Elumelu a matsayin shugaban marasa rinjaye, tare da jingine sunan Kingsley Chinda, wanda jam'iyya ke goyon baya.

Byyana sunan Elumelu ne ya fusata mambobin jam'iyyar PDP har ta kai ga sun yi barazanar dauke sandar ikon majalisar.

PDP na zargin mambobin da ta kora da hada kai da shugabancin majalisa da wasu mambobin mabalisar daga jam'iyyun adawa domin murde kujerar shugaban marasa rinjaye daga hannun wanda uwar jam'iyya ke so.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel