An kama matasa 3 da suka yi wa yar shekara 14 fyade a lokaci guda a jihar Niger

An kama matasa 3 da suka yi wa yar shekara 14 fyade a lokaci guda a jihar Niger

Rundunar yan sandan jihar Niger sun kama wasu matasa uku, Abdulrahman Ahmed mai shekara 19; Isyaku Umar mai shekara 20; da kuma Adamu Sani mai shekara 20, kan zargin yi wa yarinyar yar shekara 14 fyade.

Lamarin ya afku ne a yankin Maitumbi da ke Minna, babbar birnin jihar.

Da yake tabbatar da kamun nasu, kakakin yan sandan jihar, Mohammed Abubakar, yace matasan sun yi garkuwa da yarinyar ne a lokacin da aka aike ta sannan suka yi mata fyade.

An sanar wa da Mahaifiyar yarinyar abunda ya afku da yar’ta sannan ita kuma ta kai kara ofishin yan sanda.

Abubakar ya kara da cewa wadanda ake zargin sun amsa laifinsu sannan kuma cewa ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotu.

KU KARANTA KUMA: Da zafi-zafi: Buhari ya sake nada Boss Mustapha da Abba Kyari a matsayin sakataren tarayya da Shugaban ma’aikatansa

A wani labarin kuma, mun ji cewa a jiya Alhamis 4 ga watan Yuli 2019 ofishin hukumar hana cin hanci da rashawa (EFCC) dake a Ibadan, yayi nasara, bayan da mai shari’a Ibrahim Watilat ta babbar kotun gwamnatin tarayya dake a Abeokuta, jihar Oyo, ta kama wani Ahmed Oladimeji da laifin da hukumar ke tuhumarsa da shi.

An kama Ahmed Oladimeji da laifin tura hotunan batsa da na tsiraici ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa.

Laifin ya saba ma sashe na 24 (1)(a) da sashe na 24 (1)(b) na dokar hana laifi ta yanar gizo wadda akayi a shekarar 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel