Sharrin siyasa ya sa wasu masu son-rai ke sukar Abba Kyari – CUCGGA

Sharrin siyasa ya sa wasu masu son-rai ke sukar Abba Kyari – CUCGGA

Ku na sane cewa a cikin ‘yan kwanakin nan, an samu wasu jama’a da su ke ta faman yin ca a kan Abba Kyari wanda shi ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wata kungiya mai zaman kan-ta, ta fito ta kare babban Hadimin shugaba Buhari, inda ta ce wasu masu hamayya ne kurum su ka shirya wannan danyen aiki domin cin ma burinsu na siyasa.

Kungiyar Citizens United for Good Governance and Accountability (CUGGA) ta yi tir da yadda wasu ke kokarin batawa Abba Kyari suna duk da irin namijin kokarin da ya ke yi a bakin aiki.

CUGGA ta bayyana wannan ne a lokacin da ta kira wani zama da Manema labarai a Abuja a Ranar 3 ga Watan Yuni, 2019. Kungiyar ta ce babi ribar da za a ci wajen caccakar Malam Abba Kyari.

Shugabannin wannan kungiyar, Chinwoke Aduba da Musa Adamu sun bayyana cewa masu sukar Abba Kyari, ba su san ainihin abin da aikinsa na kare lafiya da ofishin shugaban kasa ya kunsa ba.

KU KARANTA: Rikicin da ya barkowa APC ya sa Sarki ya sa labule da Buhari

Kungiyar ta bada shawarar cewa:

“Ya kamata masu surutu a kan Kyari su koma su karanta littafin nan mai suna Gatekeepers: "How the White House Chiefs of Staff Define Every Presidency" da Chris Whipple ya rubuta a Amurka.”

Har wa yau kungiyar ta ce babu yadda mutum irin Abba Kyari wanda ya yi Digirinsa na farko a Jami’ar Warwick da kuma Digirgir a shari’a a Jami’ar nan ta Cambridge ya zama bai san aiki ba.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, wannan kungiya ta sake tunawa masu sukar babban Mukarrabin shugaban kasar da cewa ta kai har kwas ya yi a Jami’ar Harvard da a ke ji da ita.

Musa Adamu wanda tsohon ‘dan majalisa ne a jamhuriyya ta uku, ya nemi masu zargin Kyari da bai san aiki ba, su kyale shi ya cigaba da abin da aka sa shi na kare ofishin shugaban kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel