Da zafi-zafi: Buhari ya sake nada Boss Mustapha da Abba Kyari a matsayin sakataren tarayya da Shugaban ma’aikatansa

Da zafi-zafi: Buhari ya sake nada Boss Mustapha da Abba Kyari a matsayin sakataren tarayya da Shugaban ma’aikatansa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake nadin Mista Boss Mustapha a matsayin babban sakataren gwamnatin tarayya.

Shugaban kasar ya kuma amince da Malam Abba Kyari a matsayin Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa.

Hakan na kunshe ne a wani jawabi da babban mai ba Shugaban kasa shawara a kafofin watsa, labarai Garba Shehu ya saki.

A cewarsa nadin nasu su biyun ya fara aiki ne daga ranar 29 ga watan Mayu 2019.

Ga fasarar yadda ya wallafa a shafinsa na twitter: "Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake nada Mista Boss Mustapha a matsayin sakataren gwamnatin tarayya, da kuma Malam Abba Kyari a matsayin shugaban ma'aikatan shugaban kasar."

KU KARANTA KUMA: An gurfanar da malamin Islamiya da ya yi wa yarinya fyade a gaban kotu

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) karkashin inuwar Concerned APC National Stakeholders (CANS) sun yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dakatar da da Abba Kyari, Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa.

Domin matsin lamba kan bukatarsu, mambobin CANS sun mamaye fadar Shugaban kasa a ranar Litinin, 24 ga watan Yuni.

Musamman suka bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya karbi ragamar gwamnatinsa daga hannun na kewaye dashi yayinda ya fara mulki a zango na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel