El-Rufai ya nada Abdullahi a matsayin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati

El-Rufai ya nada Abdullahi a matsayin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya nada tsohon kwamishinansa na Tsare-tsare da kasafin kudi, Muhammad Sani Abdullahi a matsayin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati wato 'Chief of Staff (COS).

An bayyana nadin ne cikin wata sanarwa mai aka wallafa a shafin Twitter na gwamnan jihar Kaduna.

An nada shi kwamishina ne a 2015 a lokacin shine mafi kuruciya cikin kwamishinonin gwamnan.

DUBA WANNAN: An gano yarjejeniyar da aka kula tsakanin Goje da Shugaba Buhari kafin ya janye takararsa

Gwamnan ya kuma amince da nadin wasu mutane bakwai cikinsu har da shugabanin Cibiyar Kula da Lafiya Bai Daya (SPHCDA) da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na Jihar (SEMA).

Ga jerin sunayen wadanda aka yi wa nadin da mukamansu:

Bala Yunusa Mohammed a matsayin mataimakin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, Hamza Abubakar a matsayin Shugaban SPHCDA, Ben Kure a matsayin mai bayar da shawara na musamman kan harkokin siyasa, Maimuna Abubakar Zakari a matsayin Shugaban Hukumar SEMA sai Jamilu Albani a matsayin Direkta Janar na Harkokin Addinai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel