An gurfanar da malamin Islamiya da ya yi wa yarinya fyade a gaban kotu

An gurfanar da malamin Islamiya da ya yi wa yarinya fyade a gaban kotu

A ranar Alhamis, 4 ga watan Yuli ne aka gurfanar da wani malamin makarantar Islamiya, Habeebulah Abdulrahman a gaban alkali, bayan zarginsa da ake yi wa yarinya ‘yar shekara 16 fyade.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an gurfanar da malamin ne Kotun Majistare ta Ede da ke Jihar Osun.

Dama dai tun a ranar Litinin ne ‘yan sanda suka kama shi, sannan suka tsare shi sashin bincike na CID.

An tattaro yadda Alfa Abdulrahman wanda aka fi sani da Al-Edewy ya yi wa dalibar Islamiyyar sa fyade a garin Ede, Jihar Osun.

Yayin da Alfa Al-Edewy bai yi tantamar kwanciya da yarinyar ba, sai dai kuma ya kafe kan cewa lallai ya aure ta tun kafin ya kwanta da ita a karo na farko.

Sai dai kuma malamin ya kasa gabatar da kwakwaran shaida, domin iyayen yarinyar da ita yarinyar kan ta, duk sun karyata zancen aure a tsakanin sa da ita.

An gurfanar da shi a kotu, amma an bayar da belin sa a bisa ka’idar cewa sai ya cika sharuddan beli, wanda ya hada da mai belin ya zama ma’aikacin gwamnati mai mataki na 12, kuma ya kasance ya na da gidan kan sa, ba mazaunin gidan haya ba ne.

KU KARANTA KUMA: Hukuncin kotun koli: Adeleke yayi martani, yayi wa Oyetola fatan alkhairi

Tuni dai aka karbi belin sa tun a jiya Alhamis.

Yayin da za a ci gaba da shari’a cikin watan Agusta, an tattaro cewa iyalan Alfa din sun a ta matsa-lamba ga iyayen yarinyar su dubi girman Allah a sasanta maganar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel