Hukuncin kotun koli bai nufin karshen siyasar Adeleke, inji Atiku

Hukuncin kotun koli bai nufin karshen siyasar Adeleke, inji Atiku

-Atiku Abubakar ya yi jawabi game da shari'ar kotun koli kan zaben gwamnan Osun a ranar Juma'a

-Tsohon mataimakin shugaban kasan ya fadi cewa har yanzu jama'ar jihar Osun na kaunar Sanata Adeleke shi da jam'iyyarsa

Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin PDP, Atiku Abubakar ya tofa albarkacin bakinsa kan hukuncin da kotun koli ta yanke ranar Juma’a game da zaben gwamnan jihar Osun.

Hukuncin kotun ya tabbatar da Gboyega Oyetola a matsayin gwamnan jihar Osun yayin da kujerar ta kara yi wa Ademola Adeleke nisa.

KU KARANTA:Da duminsa: APC tayi tsokaci kan nasarar da Oyetola ya samu a kotun koli

Jim kadan bayan da kotun ta sanar da hukuncita, Atiku ya yi bayanin cewa sake tabbatar da nasarar Oyetola a matsayin wanda lashe zabe ba karshen siyasar Adeleke bane, ko kuma jam’iyyarsa ta PDP a jihar Osun.

A cewar Atiku wanda a halin yanzu yake kalubalantar zaben Shugaba Buhari a kotu ya ce: “ Duk da hukuncin da kotun kolin ta yanke, jama’ar jihar Osun na kaunar Sanata Adeleke da kuma jam’iyyar PDP, abu ne wanda ba zai taba canzawa ba.”

Jastis Rhodes Vivour na kotun kolin ne ya yanke wannan hukuncin a ranar Juma’a. Inda ta tabbatar da Gboyega Oyetola a matsayin haqiqanin wanda lashe zaben ranar 9 ga watan Maris, 2019.

A lokacin da ake gudanar da shari’ar, mutum biyar daga cikin alkalai bakwai na kotun kolin ne suka goyi bayan Oyetola a don haka kotu ta tabbatar da nasararsa.

Amma sai dai, Atiku ya ce: “ Duk da cewa an yanke hukunci kuma Adeleke bai yi nasara ba, har yanzu al’ummar jihar Osun su na mararin Adeleke.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel