EFCC ta kwace wayar i-Phone da gwalgwalai na biliyan 14 daga wajen tsohuwar minista

EFCC ta kwace wayar i-Phone da gwalgwalai na biliyan 14 daga wajen tsohuwar minista

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a jahar Legas ta bara umarnin kwace wasu tarin gwala gwalai da kuma wayar hannu samfurin I-Phone da tsohuwar ministar man fetir, Diezani Allison Maduekwe ta saya, tare da mikasu ga gwamnatin tarayya.

Hukumar EFCC ta nemi kotun ta baiwa gwamnatin tarayya daman rike kayayyakin ne sakamakon tana zargin tsohuwar ministar a gwamnatin Goodluck Jonathan ta sayesu ne da kudaden sata.

KU KARANTA: Ministocin Buhari: Abin da yasa har yanzu aka ji shiru – Faruk Adamu Aliyu

Lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo ya shaida ma kotun cewa kayayyakin sun hada da wayar hannu kirar I-Phone, gwala gwalai da suka hada da dan kunnaye, sarkoki, agoguna, da sauransu, inda yace darajarsu gaba daya ya haura dala miliyan 40, kimanin naira biliyan 14 kenan.

Bayan sauraron bukatar lauyan EFCC, sai Alkalin kotun, mai sharia Nicholas Oweibo ya yanke hukuncin mika dukkanin kayayyakin arzikin zuwa ga hannun gwamnatin tarayya a matakin wucin gadi, zuwa lokacin da tsohuwar ministan za ta amsa sammaci.

Har yanzu dai Diezani na kasar Ingila ta ki yarda ta dawo Najeriya domin amsa dimbin kararrakin da hukumar EFCC ke mata da suka danganci satar biliyoyin kudaden gwamnati a zamanin da take rike da mukamin ministar man fetir.

Kuma duk kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na ganin kasar Birtaniya ta mika mata tsohuwar ministan, hakan ya ci tura, bisa wannan dalili ne alamu ke nuna ba lallai ta dawo Najeriya a zamanin mulkin shugaba Buhari ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel