Nasara a kotun koli: Buhari ya taya gwamnan jahar Osun murna

Nasara a kotun koli: Buhari ya taya gwamnan jahar Osun murna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na daga cikin yan gaba gaba da suka fara taya gwamnan jahar Osun, Gwamna Gboyega Oyetola murnar samun nasara a shari’ar daya fafata da Sanata Ademola Adelele a kotun koli.

Legit.ng ta ruwaito shugaba Buhari ya bayyana farin cikinsa da nasarar da gwamnan jam’iyyarsu ta APC ya samu ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani, Twitter, jim kadan bayan kotun koli ta yi watsi da karar da dan takarar PDP, Sanata Adeleke ya shigar gabanta.

KU KARANTA: Ministocin Buhari: Abin da yasa har yanzu aka ji shiru – Faruk Adamu Aliyu

“Hukuncin kotun koli ya kawo karshen tirka tirkar da aka dade ana yi akan zaben gwamnan jahar Osun daya gudana a shekarar 2018, kuma hakan ya kawar da duk wasu kalubale dake gaban gwamnan wajen ciyar da jahar Osun gaba.

“Na jinjina ma jama’an jahar Osun ta yadda suka kyale tsarin doka da oda ya yi aikinsa tun daga farkon shari’ar har zuwa yanzu, don haka nake kira ga Gwamna Oyetola da jam’iyyar APC dasu fara aiki tukuru don ganin su janyo kowa a jiki.” Inji shi.

Daga karshe Buhari yace gwamnatinsa za ta cigaba da hada kai da gwamnatin jahar Osun don samar da baben more rayuwa da cigaban arziki ga jama’an jahar Osun gaba daya.

A ranar juma’a, 5 ga watan Yuli ne Alkalan kotun kolin Najeriya suka tabattar da nasarar da gwamnan jahar Osun na jam’iyyar APC, Adeboyega Oyetola ya samu a zaben gwamnan jahar daya gudana a ranar 22 ga watan Satumbar shekarar 2018.

Dan takarar jam’iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke ne ya daukaka kara zuwa kotun kolin inda yake kalubalantar nasarar abokin takarar tasa, haka zalika yana kalulabalantar hukuncin kotun daukaka kara data tabbatar da nasarar Oyetola.

Sai dai a zaman kotun na ranar Juma’a, 5 ga watan Yuli, Alkalai biyar cikin Alkalai bakwai da suka zauna sun tabbatar da nasarar Gwamna Oyetola, kamar yadda jagoransu, mai sharia Bode Rhodes-Vivour ya bayyana, yayin da mai sharia Kumai Akaah da Paul Galinje suka yi bara’a da hukuncin abokan aikinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel