Masarautar Kano Zata tura kudiri zuwa majalisa mai shafi 218

Masarautar Kano Zata tura kudiri zuwa majalisa mai shafi 218

-Sarki Muhammadu Sanusi II ya shirya wani kudiri da zai duba lamarin zamantakewar iyali don magance matsalolin auren wuri, saki da almajiranci

-Shugaban kwamitin lafiya na masarautar Kano ne ya bayyana haka

-Ya kuma bayyana cewa tuni ma sarki Sanusi ya mika kudirin ga gwamna Ganduje don a tura shi zuwa majalisa

Masarautar Kano, karkashin jagoranci Sarki Muhammadu Sanusi II ta shirya wani kudiri da zai duba lamarin zamantakewar iyali don magance matsalolin auren wuri, sakin aure da kuma almajiranci a jihar.

Wannan kudirin dai har an mika shi zuwa ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje don ya aika zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano don tabbatar da shi ya zama doka.

Shugaban kwamitin masarautar Kano akan harkokin lafiya, Dr. Bashir Muhammad ne ya bayyana haka a wani taro da aka gudanar a jihar Kaduna

Ya bayyana cewa ya dauki masarautar da wasu masu ruwa da tsaki tsawon shekara biyu don tsara wannan kudiri mai shafi 218. Ya kuma bayyana cewa idan aka tabbatar da kudirin ya zama doka, to zai taimaka wajen magance matsalolin zamantakewa musamman auren ‘ya’ya mata da kuma almajiranci.

KARANTA WANNAN: Kaduna: PDP za ta daukaka kara kan nasarar da El-Rufai ya samu a kotu

Ya bayyana cewa “Eh akwai kudirin da mai martaba sarki Kano Sanusi ya shirya akan zamantakewar iyali kuma har ya mika shi zuwa ga gwamna don a isar da shi majalisa.”

“Dokar ta kare duk wani hakkin aure a musulunci bisa shari’ah, misali, an sanya ka’idojin da mutum zai cika kafin a bashi aure, dan gane da mata kuma, izuwa shekara nawa ne za a iya bada su aure” A cewarshi.

Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya akan hubbasa da ta yi na magance matsalar almajiranci a arewacin Najeriya.

Da yake maida jawabi, wani mai rike da sarautar gargajiya daga jihar Kano, Yahaya Inuwa Abbas ya bukaci iyaye da su rinka saka ‘ya’yansu mata a makarantun koyan aikin asibiti don su zama ma’aikatan asibiti.

Ya bayyana cewa yana da kyau ‘ya mace ta samu wannan ilimin domin ta zama malamar asibiti ko kuma unguwar zoma. Ya bayyana cewa wannan ilimin na mata yana da matukar mahimmanci ga al’umma.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel