Tirkashi: 'Yan bindiga sunyi garkuwa da wasu turawa guda biyu, sun kuma kashe dan sandan da yake gadinsu

Tirkashi: 'Yan bindiga sunyi garkuwa da wasu turawa guda biyu, sun kuma kashe dan sandan da yake gadinsu

- Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wasu 'yan kasar China mutum biyu

- 'Yan Chinese din suna aiki ne a wani kamfani na sarrafa gilashi dake jihar Edo

- 'Yan bindigar sun kashe wani dan sanda da yake gadin 'yan China din kafin su gudu dasu

Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindiga sunyi awon gaba da wasu 'yan chinese guda biyu da suke aiki da wani kamfanin sarrafa gilashi, a jihar Edo.

Lamarin ya faru ranar Larabar nan da ta gabata a kauyen Utesi akan hanyar Benin zuwa Auchi. A yadda rahoton ya bayyana, dan sandan da aka saka yake gadin turawan ya rasa ransa yayin musayar wuta da 'yan bindigar.

An bayyana cewa turawan suna kan hanyarsu ta zuwa gida, yayin da suka tashi daga gurin aiki, kawai sai suka ga 'yan bindigar sun rufe hanyar, daga nan suka dauke su bayan sun kashe dan sandan dake gadinsu.

KU KARANTA: Wannan abin dariya da yawa yake: An gurfanar da wani Zakara a gaban kotu, saboda yana damun mutane da cara

Da yake magana da manema labarai, wani wanda ya bukaci a boye sunansa ya ce:

"Turawan na fitowa daga cikin kamfanin, dama 'yan bindigar suna jiransu, kawai sai suka fara harbinsu, 'yan bindigar sun kashe dan sandan, daga nan suka gudu da 'yan Chinese din."

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Dan Malam Muhammed, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace an kai musu rahoton faruwar lamarin ranar Laraba. Yanzu haka kuma muna iya bakin kokarin mu domin ganin mun ceto rayuwarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel