Zaben Zamfara: Kotun korafin zabe ta dage sauraron karar zaben Gwamna

Zaben Zamfara: Kotun korafin zabe ta dage sauraron karar zaben Gwamna

-Kotun sauraron korafin zabe ta jihar Zamfara ta dage sauraron karar zaben gwamna zuwa ranar da ba'a riga a sanar da ita ba yanzu

-Jastis Fatima Zubairu ce ta dage wannan karar bayan da ta aimnta da rokon da wakilan jam'iyyar APP a kotun suka neman domin sake kimtsawa karar

Kotun sauraron korafe-korafen zabe ta jihar Zamfara a ranar Juma’a ta dage sauraron karar dake kalubalantar nasarar Bello Matawalle na jam’iyyar PDP.

Mutane biyu wadanda ke wakiltar jam’iyyar Action People’s Party wato APP a kotun, Farfesa Agbo Madaki da Mista Obed Agu su ne suka nemi a dage wannan karar domin su samu damar shirya ma ta.

KU KARANTA:Lawan ya roki Kungiyar kwadagon Najeriya da ta janye maganar yajin aiki

Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa, Alhaji Zayyanu Salisu na APP shi ne jigon shigar da karar inda yake neman kotun ta yi watsi da zaben gwamnan jihar Zamfara wanda Bello Matawalle na PDP ya lashe.

A cikin karar ta sa mai lamba EPT/ZM/GOV/2019, Zayyanu yana tuhumar jam’iyyar PDP da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC.

Jastis Fatima Zubairu wadda ke jagorantar shari’ar ta dage karar kamar yadda Madaki da Agu suka nema zuwa ranar da ta ce za’a sanar da ita nan bada jimawa ba.

Fatima ta ce: “ Rokon na dage karar ya samu karbuwa kuma kwanan nan zamu sanar da bangarorin ranar da za su dawo domin a cigaba da shari’a.”

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya tattaro mana bayanan cewa, a ranar 1 ga watan Yuli ne tawagar lauyoyin dake wakiltar Salisu na jam’iyyar APP suka nemi wannan bukatar a wurin kotun.

Haka zalika, bangaren dake wakiltar Salisu ya bukaci wannan damar ne domin sake tattaro hujjoji tare da gamsassun bayanai wadanda za su sa a soke zaben gwamnan 9 ga watan Maris, 2019 na Zamfara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel