Da duminsa: APC tayi tsokaci kan nasarar da Oyetola ya samu a kotun koli

Da duminsa: APC tayi tsokaci kan nasarar da Oyetola ya samu a kotun koli

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Osun ta bayyana hukuncin da kotun koli ta zartar na tabbatar da nasarar Gwamna Gboyega Oyetola a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna na ranar 22 ga watan Satumba a matsayin abin tarihi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ta ruwaito cewa kotun ta zartar da hukuncin amincewa da nasarar Oyetola ne inda alkalai biyar cikin bakwai suka rinjaye biyu da ba su amince da hukuncin ba.

A cikin jawabin da Sakataren ta na jihar, Mista Kunle Oyatomi ya fitar a ranar Juma'a a Osogbo, ya ce Allah ya yi amfani da kotu mafi girma a kasar ya bayyana gaskiya cewa Oyetola ne ya lashe zabe.

DUBA WANNAN: An gano yarjejeniyar da aka kula tsakanin Goje da Shugaba Buhari kafin ya janye takararsa

A cewarsa, Allan da al'ummar Osun su ke bautawa ya amsa addu'o'insu ya basu shugaban da suke so.

"Tsoron mu shine irin bala'in da zai afkawa mutanen jihar Osun idan da ace PDP ce tayi nasara.

"Munyi matukar murna bisa wannan rahamar da Allah ya yi mana.

"Wadanda ke fatan ganin wata hukunci da ba wannan ba sun koyi darasi cewa ramin karya kurarre ne.

"PDP ne suka yi kokarin kawo tashin hankali kan zaben da aka gudanar a watan Satumba."

Oyatomi ya ce duk makircin da aka kula a kotun daukaka kara ta kare a kotun koli.

"Yanzu wannan ya zama tarihi. Wannan ba nasarar jam'iyyar APC bane kawai; nasara ce ta mutanen jihar Osun.

"Muna addu'ar Allah ya bawa gwamnan hikima da hangen nesa da karfin cigaba da ayyukan alheri da ya gada kuma ya aikata ayyukan da mutanen Osun za suyi alfahari da su," inji Oyotomi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel