Hukuncin kotun koli: Adeleke yayi martani, yayi wa Oyetola fatan alkhairi

Hukuncin kotun koli: Adeleke yayi martani, yayi wa Oyetola fatan alkhairi

Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya yi martani akan kaye da ya sha a kotun koli cewa yana yi wa Gwamna Gboyega Oyetola fatan alkhairi.

Yayinda yake taya Oyetola murnar nasararsa a kotun koli, Adeleke ya tabbatar da cewa kudirinsa na son zama gwamnan Osun ba abun a mutu ko a ayi rai bane.

A wani jawabi da ya gabatar bayan hukuncin kotu, Sanata Adeleke yace kotun koli ce mafi girma a kasar sannan a matsayinsa na dan kasa mai bin doka, zai bi hukuncin kotun sannan ya mutunta duk kuwa da yadda aka yi.

Ya kuma jinjinawa abunda ya kira a matsayin jajircewar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar don ganin sun tabbatar da damokradiyya kamar yadda dukkaninsu suka shige masa gaba.

KU KARANTA KUMA: Kaduna: PDP za ta daukaka kara kan nasarar da El-Rufai ya samu a kotu

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Alkalan kotun kolin Najeriya sun tabattar da nasarar da gwamnan jahar Osun na jam’iyyar APC, Adeboyega Oyetola ya samu a zaben gwamnan jahar daya gudana a ranar 22 ga watan Satumbar shekarar 2018.

Dan takarar jam’iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke ne ya daukaka kara zuwa kotun kolin inda yake kalubalantar nasarar abokin takarar tasa, haka zalika yana kalulabalantar hukuncin kotun daukaka kara data tabbatar da nasarar Oyetola.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel