Kaduna: PDP za ta daukaka kara kan nasarar da El-Rufai ya samu a kotu

Kaduna: PDP za ta daukaka kara kan nasarar da El-Rufai ya samu a kotu

Kotun sauraron karrakin zabe na jihar Kaduna, a ranar Alhamis ta hana wani kwarare da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta gabatarwa kotu domin ya bayar da shaida kan zabe saboda kurewar wa'adin gabatar da shaidu.

Shugaban kotun zaben, Justice Ibrahim Bako ya ce ba za a bawa shaidan damar yin magana a kotun ba saboda wa'addin kwanaki 14 da aka basu na gabatar da shaidan ya shude.

An gayyato kwarraren ne domin ya bayar da shaida kan wasu kayayakin zabe da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC tayi amfani da su yayin zaben gwamna da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris a Kaduna.

DUBA WANNAN: Kannywood: Adam Zango ya nuna sabuwar babbar mota ta miliyan N23m da ya saya

Lauyoyin jam'iyyar APC da INEC sun ki amincewa da mai bayar da shaidan da jam'iyyar PDP da dan takarar gwamnan ta Alhaji Isah Ashiru suka gabatarwa kotun zaben.

Lauyoyin biyu sun fadawa kotun cewa an sanar da su cewa za a gabatar da mai bayar da shaidan ne daf da za a fara sauraron shari'ar.

Sun ce suna bukatar lokaci domin suyi nazarin takardar su kuma shirya irin tambayoyin da za si yi wa mai bayar da shaidan hakan ya sa suka bukaci kotu da hana shi bayar da shaidan.

A bangarensa, Justice Bako ya ce ba za a bari mai bayar da shaidan ya yi magana a kotun ba saboda masu shigar da karar ba su gabatar da shi cikin wa'adin lokacin da aka diba musu ba.

Lauya mai kare Gwamna Nasir El-Rufai, Abdulhakeem Mustapha (SAN) ya shaidawa manema labarai cewa kotun ta bawa masu shigar da karar wa'adin kwanaki 14 su gabatar da masu bayar da shaidun su.

Lauyan mai shigar da kara, Elisha Kurah (SAN) ya shaidawa manema labarai cewa zai daukaka kara kan hana su gabatar da mai bayar da shaidan su.

"Mun kawo kwarare domin ya bayar da shaida amma kotun ta ce ba za ta amince da shi ba.

"Muna ganin hakan ba dai-dai bane saboda haka za mu daukaka kara," inji Kurah.

Kotun ta dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 15 ga watan Yuli domin sauraran shaidun El-Rufai, APC da kuma Hukumar INEC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel