Majalisar dokoki ta sha alwashin sanya baki kan ci gaba da tsare El-Zakzaky

Majalisar dokoki ta sha alwashin sanya baki kan ci gaba da tsare El-Zakzaky

- Mambobin majalisan dokokin kasa sun yi martani akan zanga-zangar da kungiyan Shi’a tayi kan cigaba da tsare shugabanta, Ibraheem El zakzaky

- Shugaban masu rinjayi a majalisa, Alhassan Doguwa ya sha alwashin shiga cikin lamarin tsare Zakzaky

- Jagoran kungiyar masu zanga-zangan yayi zargin cewa lafiyar shugabansu na dada tabarbarewa sannan cewa yana bukatar kulawar gaggawa

Majalisan dokokin kasa ta sha alwashin sanya baki cikin lamarin cigaba da tsare Shugaban ku ngiyar Shi’a, Ibraheem El Zakzaky.

El-Zakzaky ya kasance a tsare tsawon watanni da dama bayan rikici da ya barke tsakanin mabiyansa da rundunan sojin Najeriya.

A cewar rahoton wata gidan talabijan, shugaban masu rinjaye a majalisar , Alhassan Doguwa ya dau alkawarin ne yayin da yake gabatar da jawabi ga mambobin kungiyar da suka gudanar da zanga-zangan a harabar majalisan dokokin kasa da ke Abuja.

Jagoran kungiyar masu zanga-zangan yayi zargin cewa lafiyar shugabansu na dada tabarbarewa sannan cewa yana bukatar kulawar gaggawa. Abdullahi Musa tare da suran masu zanga - zangan suna kira akan a sake shi.

KU KARANTA KUMA: Daga karshe majalisar wakilai ta magance rikicin da ya kunno kai kan zabin shugabanninta – Jibrin ya tabbata

Legit.ng ta rahoto a baya cewa wani mai kare hakkin dan adam kuma babban lauyan Najeriya (SAN), Femi Falana, ya bukaci IMN wacce aka fi sani da Shi’a, dasu cigaba da yin zanga - zanga akan batun sakin El-Zakzaky.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel