Yanzu Yanzu: INEC ta tafka magudi a zaben gwamnan Osun - Alkalin Kotun Koli

Yanzu Yanzu: INEC ta tafka magudi a zaben gwamnan Osun - Alkalin Kotun Koli

Wani Alkalin Kotun Koli da bai amince da hukuncin da kotun ta zartar kan zaben Gboyega Oyetola a matsayin gwamnan jihar Osun ya zargi Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC da tafka magudi a zaben.

Alkalai biyu, Kumai Akaas da Paul Galinje sun ce ba su amince hukuncin da aka zartar na tabbatar da nasara Mista Oyetola na jam'iyyar APC ba.

Justice Akaas ya zargi INEC ta tafka magudin zabe yayin zaben raba gardama da aka gudanar yayin da Justice Galinge ya ce ya dace kotu ta mayar da hankali kan zargin magudin da aka ce anyi yayin zaben raba gardamar.

DUBA WANNAN: Kannywood: Adam Zango ya nuna sabuwar babbar mota ta miliyan N23m da ya saya

Mr Akaas ya ce INEC ta ba da wani kwakwaran dalili na yin zaben raba gardama tun farko.

"Kamata ya yi INEC ta zama alkali ba ta nuna fifiko ba. Tun lokacin da INEC ta ce zaben bai kammalu ba alama ce da ke nuna tana shirya wani makarkashiya. Kuma ta nuna hakan yayin zaben raba gardamar," a cewar Mr Akaas cikin bacin rai.

Alkalin sun nuna bacin ransu ne kan hukuncin da kotun koli ta yanke kan karar da Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP ya shigar.

Alkalai biyu cikin bakwai da suka saurari karar sun nuna kin amincewarsu da tattabarwa Mr Oyetola nasarar lashe zaben gwamnan da aka gudanar a watan Satumban 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel