Daga karshe majalisar wakilai ta magance rikicin da ya kunno kai kan zabin shugabanninta – Jibrin ya tabbatar

Daga karshe majalisar wakilai ta magance rikicin da ya kunno kai kan zabin shugabanninta – Jibrin ya tabbatar

Daga karshe majalisar wakilai ta magance rikicin da ya kunno kai a cikinta akan nadin Shugaban marasa rinjaye a majalisar karkashin jagorancin kakakin majalisa Femi Gbajabiamila.

Jigon majalisar wakilai kuma na kusa da Gbajabiamila, Hon. Abdulmumin Jibrin ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 5 ga watan Yuli.

“Komai ya daidaita a majalisar wakilai. An daidaita wajen rabe-raben manyan mukaman majalisar.

“Yan sa’o’i da suka gabata aka daidaita lamarin. Muna godiya ga dukkanin takwarorinmu kan goyon bayansu da kuma wadanda suka fusata kan fahimtarsu,” inji shi.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, rigimar da aka fara a majalisar wakilai a ranar Laraba, 3 ga watan Yuli ya ci gaba yayinda kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya amince da ci gaba da zaman majalisa daga inda aka kwana.

KU KARANTA KUMA: Ministocin Buhari: Abin da yasa har yanzu aka ji shiru – Faruk Adamu Aliyu

Hon. Kingsley Ogundu Chinda mai wakiltan mazabar Obio/Akpor, jihar Rivers yayi kokarin yin jawabi amma kakakin majalisar yaki bashi dama kan cewa bai zauna a kan kujerar da aka basa ba.

Gbajabiamila ya bukai yan majalisar da su lura da oda ta 9 doka ta 4 da kuma oda ta 10 na tsarin majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel