Yanzu Yanzu: Hukumar yan sanda ta bayar da belin Sanata Elisha Abbo

Yanzu Yanzu: Hukumar yan sanda ta bayar da belin Sanata Elisha Abbo

Rundunar yan sandan Najeriya ta saki sanata mai wakiltan Adamawa ta arewa, Elisha Abbo akan beli. Yan sandan birnin tarayya sun saki Abbo bayan tsare shi da aka yi kan zargin cin zarafi n wata mai jego a kantin siyar da kayan jima’i a Abuja.

PRNigeria ta ruwaito cewa an saki Abbo a safiyar ranar Juma’a, 5 ga watan Yuli bayan ya shafe tsawon sa’o’i 24 a hannun yan sandan birnin tarayya.

An kuma tattaro cewa Abbo da kansa ne ya gabatar da kansa ga hukumar yan sanda domin bincike a cikin lamarin wanda ya haddasa cece-kuce a fadin kasar baki daya.

Har ila yau wasu majiyoyi na yan sanda sun bayyana cewa da fari ba a ba sanatan beli ba bayan amsa tambayoyi daga yan sandan.

Majiyar tace an ba Abbo beli ne kawai saboda matar da ya ci zarafi bata nan domin tabbatarwa da kuma bayar da nata bangaren na labarin.

KU KARANTA KUMA: Zaben gwamnan Kano: Halin da ake ciki a zaman karshe da kotu tayi kan shari’ar Ganduje da Abba gida-gida

A cewar majiyar, matar da sanata Abbo ya ci zarafi ta yi tafiya domin halartan bikin mutuwa na wani dan uwanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel