Zulum sai ya ce banyi komi ba a fagen aiki – Shettima

Zulum sai ya ce banyi komi ba a fagen aiki – Shettima

-Tsohon gwamnan Borno, Sanata Kashim Shettima ya bayyana gwamnan jihar na yanzu Babagana Umara Zulum a matsayin agogo sarki aiki

-Kashim Shettima ya fadi wannan zancen ne bayan da aka kammala zaman majalisar dokoki inda yake cewa yana sa ran Zulum zai zarce shi a fagen aiki

Tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima ya ce magajinsa kan kujerar gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum zai yi aikin da yafi nasa.

Shettima wanda a yanzu ke wakiltar Borno ta Tsakiya a majalisar dattawa, ya fadi wannan maganar ne bayan an kammala zaman majalisar dokoki a jiya Alhamis, inda yake cewa, “ Ni banyi mamakin ganin ayyukan da Zulum yayi cikin kwanaki 35 dinsa na farko a ofis ba.”

KU KARANTA:Abinda shugabannin tsaro suka tattauna da Shugaba Buhari

“ Na karanta a rubuce wasu kuma na ji da kunne na mutane na fadin kyawawan kalamai game da ayyukan da gwamnan yayi ciki kwanaki 35 kacal.

“ Mutane na mamakin yadda gwamnan a cikin awa 24 ya iya ganawa da kungiyar tsaron JTF da ta mafarauta kana kuma ya kara masu alawus nan take. Har ila yau gwamnan ya ba su karin motocin yin zirga-zirga domin sauwake masu aikin na su.

“Haka zalika, Zulum ya yi ganawar ke-ke da ke-ke da Shugaba Buhari inda suka tattauna sha’anin tsaron Jihar Borno duk a cikin awa 24.” A cewar Shettima.

Sanatan ya cigaba da jero zancensa, inda yake cewa, mutane na cike da mamakin abubuwan da gwamnan yayi cikin kwanaki 35. A cikin wadannan kwanakin gwamnan ya ziyarci kananan hukumomi 20 daga cikin 27 da jihar take da su, inda ya binciki yanayin makarantu, asibitoci, tituna da kuma harkar samar da ruwan sha.

Shettima ya ce: “ Mutanen da ke mamakin aikin Zulum, saninsa ne ba suyi ba, ni na dade da karantarsa domin nasan abinda zai iya yi kuma insha Allahu ina sa ran a bangaren ayyuka sai ya yi abinda ni banyi ba.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel