Hankula sun tashi a Jihar Imo yayin da makiyaya su kayi kane-kane a wata gona

Hankula sun tashi a Jihar Imo yayin da makiyaya su kayi kane-kane a wata gona

-Al'ummar Obokofia na cikin halin tashin hankali yayin da aka samu makiyaya sun yi kakagida a cikin wata gona

-Shugaba Buhari ya kira ganawa ta gaggawa da shugabannin tsaron a fadarsa dake Abuja jiya inda suka tattauna halin tsaron Najeriya

A jiya Alhamis ne Babbar kotun kasa dake Abuja ta yi watsi da karar da Kungiyar Miyetti Allah ta shigar inda take kalubalantar dokar hana yin kiwon dabbobi a fili wanda gwamnatin Jihar Binuwe ta sanya a shekarar 2017.

Gwamnan jihar Binuwe, Samuel Ortom ya bayyana hukuncin kotun a matsayin wata babbar nasara inda yake cewa, “ hukuncin nasara ce ga dimokuradiyyar Najeriya saboda an girmama doka da oda”.

KU KARANTA:Abinda shugabannin tsaro suka tattauna da Shugaba Buhari

Rahotanni sun nuna cewa, hankula sun tashi a karamar hukumar Ohaji dake jihar Imo yayin da aka samu makiyaya sun gaje wata gona kana kuma sun furta cewa babu su ba barin wannan gonar.

A ranar Laraban da ta gabata, wasu makiyaya sun firgita al’ummar yankin Obokofia na karamar hukumar Ohaji da harbe-harben bindiga, wanda kuma sun yi hakan ne domin a san cewa suna nan kuma ba su da ranar barin wurin da suke.

Har ila yau, firgici tsakanin al’umma mazauna karamar hukumar na dada karuwa, hakan ne ya sanya Shugaba Buhari ya kira ganawa ta gaggawa da shugabannin tsaron Najeriya a fadarsa jiya Alhamis. A karshen ganawar hafsun sojin sama, Abubakar Sadiq ya ce “ tsarin da suke amfani da shi yana tafiya yadda ya kamata.”

Rahotanni daga jaridar Vanguard sun ruwaito cewa, a jiya Alhamis ne al’amarin ya bude wani sabon shafi inda al’ummar Obokofia ke cikin tashin hankali kasancewar makiyayan da aka samu a yankin sun cije kan cewa sun ga wurin zama kuma ba inda za su je.

Haka zalika, shugabannin yankin sun kafa kwamiti domin kwantar da tarzomar, inda aka sanya Damian Ezeru a matsayin shugaban kwamitin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel