JAMB ta sake kama wani da ya kara makin shi daga 162 zuwa 209

JAMB ta sake kama wani da ya kara makin shi daga 162 zuwa 209

-An sake kama wani da ya kara sakamakon jarabawarsa ta share fagen shiga jam’ia daga 162 zuwa 209 da taimakon wasu yan danfara

-Wanda aka kaman, mai suna Cletus Kokowa, an samu nasarar damke shi a hedikwatar JAMB bayan da ya kai koke akan sakamakon jarabawar tasa a jiya Alhamis 4 ga watan Yuli 2019

-Kokowa ya tuntube yan danfarar ta dandalin sada zumunta na whatsapp bayan da aka gaya mashi cewa za su iya gyara mashi sakamakon daga 162 zuwa 209

Hukumar share fagen shiga jami'o'i (JAMB) ta damke wani Cletus Kokowa a bisa zarginsa da kara makin jarabawarsa ta share fagen shiga jami’a daga 162 zuwa 209 tare da taimakon wasu yan danfara.

Wannan na zuwa ne bayan da hukumar ta kama wani Adah Eche a cikin watan Yuni da aikata irin wannan laifi.

Kokowa ya amsa laifinsa ne a jiya Alhamis 4 ga watan Yuli 2019 bayan da hukumar ta kama shi inda ya bayyana cewa ya biya kudi Naira 10,000 don a kara mashi makin.

Kokowa, dan asalin jihar Bayelsa, ya tuntubi wasu yan danfara ta hanyar dandalin sada zumunta whatsapp inda aka bayyana mashi cewa za a iya kara mashi sakamakon daga 162 zuwa 209.

Amma kash, sakamakon bai canza ba shafin yanar gizo na hukumar JAMB, wanda hakan ya sanya hukumar ta bukaci mahaifin Kokowa, Garen Kokowa da ya gabatar da korafinsa a rubuce don a gyara ma dansa sakamakon.

Mahaifin ya rubuta ma hukumar cewa “Rashin daukar mataki daga wajenku don ku gyara matsalar ya sanya 'da na ya rasa gurbi a makarantar sojoji ta Najeriya.”

Ya kara da cewa “Amma ina rokonku da ku gaggauta gyara masa sakamakon ta yadda zai samu gurbin karatu a jam’iar da ya zaba ta biyu.”

Daga nan ne sai JAMB ta gayyace Kokowa Ofishinta inda ta buka ce shi da ya zo da sakamakon guda biyu a matsayin shaida, inda daga nan ne suka gane dayan sakamakon na bogi, wanda daga bisani ya amsa cewa ya sauya sakamakon.

KARANTA WANNAN: Zaben gwamnan Kano: Halin da ake ciki a zaman karshe da kotu tayi kan shari’ar Ganduje da Abba gida-gida

Kokowa ya bayyana cewa “Sun turo mani da sakon E-mail ta yanar gizo cewa za su iya taimako na su kara mani yawan makin. Daga nan sai na tura masu nambar jarabawata. Bayan da sakamakon ya fito sai na duba naga na samu 209. Daga nan sai wani cikinsu ya kirani ya ce in biya su kudin aikin.”

“Daga baya sai na duba naga 162. Na yi mamaki. Na samu labarin cewa kara maki laifi ne amma ban yarda ba. Ban fada ma babana da kawuna game da abun ba.”

Shugaban hukumar, farfesa Oloyede ya ce hukumar za ta gano duk wani wanda yayi cuta kafin jarabawar, ko lokacin da akeyi koma bayan da aka gama, kuma za kama shi a kai shi kotu.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel