Saraki da Okorocha ‘yan gaban goshin alkali ne, inji hukumar EFCC

Saraki da Okorocha ‘yan gaban goshin alkali ne, inji hukumar EFCC

-Hukumar EFCC na neman a karbe shari'ar Saraki da Okorocha daga hannun Jastis Taiwo Taiwo saboda yana nuna son kai wurin hukunci

-EFCC ta rubuta korafi mai dauke da hujjoji guda biyu inda take neman a karbe wannan kara daga hannun alkalin

-Sai dai kuwa duk da kokarin hukumar ta EFCC wurin a karbe kararar a karo na farko ba aminta da korafinta ba

Hukumar yaqi da cin hanci da kuma hana zagon kasan tattalin arziki ta EFCC na zargin Jastis Taiwo Taiwo na Babbar Kotun Abuja da nuna bangaranci da kuma son kai kan shari’ar tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da kuma tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha.

Wannan zargin na hukumar EFCC na kunshe ne a cikin korafe-korafe guda biyu wadanda hukumar ta rubuta inda take kalubalantar cancantar Jastis Taiwo a matsayin alkalin da zai yi shari’a ga Saraki da Okorocha.

KU KARANTA:Abinda shugabannin tsaro suka tattauna da Shugaba Buhari

EFCC ta ce, “ Duk da cewa bai zama lallai sai munyi nasara a koda yaushe ba, amma abinda muka sani game da Jastis Taiwo musamman wurin yanke hukunci ga shari’ar da ta shafi cin hanci shi ne muke tsoro, musamman saboda nuna bangaranci daga wajensa.”

Hukumar EFCC, da farko ta nemi a karbi shari’ar daga hannunsa, amma hakan bai samu ba saboda babban alkalin kotun Jastis Adamu Kafarati ya qi amincewa da kudurin na su.

Bugu da kari, EFCC ta fadi dalilinta guda biyu da suka sanya take neman a karbe wannan shari’a daga hannun Jastis Taiwo.

Abu na farko shi ne: “ Jagorancin shari’ar Babbban Kotun kasa dake jihar Ekiti. A wancan lokacin Jastis Taiwo ya gudanar da hukunci guda biyu, daya daga ciki shari’a ce wadda ta kunshi tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose sai na biyu wadda ta kunshi ministan shari’ar jihar na wancan lokacin.”

Kasancewar yadda shari’ar ta kasance tsakanin mutanen biyu da hukumar EFCC, shi ne bai wa hukumar dadi ba, inda take zargin alkalin da nuna son kai wurin yin hukunci musamman ga shari’ar da ta shafi cin hanci da rashawa. A karshe an dage sauraron karar zuwa 27 ga watan Satumbar 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel