Yan ta’addan Zamfara da yan kungiyar tsaro sun fara musayar mutanen da suka kama

Yan ta’addan Zamfara da yan kungiyar tsaro sun fara musayar mutanen da suka kama

-Yan kungiyar tsaro ta sa kai na jihar Zamfara da yan ta’addan jihar sun fara musayar mutanen da suka kama

-Hakan na da zummar cimma yarjejeniyar sulhu da aka kulla tsakanin jihar Zamfara da yan ta'addan

-Komishinan yan sanda na jihar ya bada tabbacin cewa zasu tsaya kai da kafafu wajen ganin an yi sulhun

Yan kungiyar tsaro ta sa kai na jihar Zamfara da yan ta’addan jihar sun fara musayar mutanen da suka kama don cimma yarjejeniyar da aka kulla akan yin sulhu.

Wasu Fulani, maza da mata da yara su 25 da yan kungiyar sa kai suka kama tun cikin watan Afirilu an mika su ga hannun komishinan yan sanda na jihar CP Usman Nagogo a fadar Sarkin Dansadau a jiya Alhamis 4 ga watan Yuli 2019.

CP Nagogo ya bayyana cewa musayar na daga cikin yarjejejinyar da aka kulla da yan ta’addan, inda ya kara da cewa, wadanda aka kaman za a mika su ga gwamna Bello Mutawalle kuma za a ajiye su a hannun hukuma har sai yan ta’adda sun sako mutanen da suka kama.

Cp Nagogo ya bayyana cewa “Ina wakiltar babban Sifeton yan sanda kuma ni da gwamna Bello Matawalle za mu iya tabbatar maku da cewa za mu tsaya ka’in da na’in wajen ganin anyi wannan sulhun. Babu yaudara cikin lamarin, shi ya sanya nike rokon masu ruwa da tsaki da su kara hakuri.”

Ya bayyana cewa ya samu hanyar sadarwa tsakaninshi da shugaban yan ta’addan kuma yana yawan tuna masu sharuddan yarjejeniyar don gudun kada su karya sharuddan.

KARANTA WANNAN: Yanzu Yanzu: Tsohon ministan PDP da dan sa sun karbi katin zama 'yan APC

Da yake maida jawabi, Sarkin Dansadau, Alhaji Hussaini Umar ya ce sulhu ita ce hanya mafi kyau don magance matsalolin tsaro, musamman satar shanu da garkuwa da mutane a jihar.

Ya bayyana cewa “Muna cikin matsanancin tashin hankali da irin kashe kashen da akeyi. Za mu cigaba da bada goyan baya dari bisa dari don ganin an yi duk wani abun da zai maido da zaman lafiya a jiharmu.”

Wasu daga cikin shugabannin yan kungiyar sa kai sun yi korafi akan karya sharuddan yarjejeniyar da aka kulla daga wajen yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta masu suka dauki makamansu don su kare kansu kasancewar da yawansu marayu ne da suka rasa iyayensu sakamakon hare haren yan ta’adda.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel