Dalilin da ya sanya nike zagaye a Kwara – Gwamna Abdulrazak

Dalilin da ya sanya nike zagaye a Kwara – Gwamna Abdulrazak

-Gwamnan jihar Kwara ya bayyana cewa byana zagaye a ma'aikatun gwamnati don ya ga kalubalen da ke gabanshi

-Gwamna AbdulRazaq ya bayyana cewa yana sane da cewa lalacewar al'amurra a jihar ta kai intaha, amma dai yafi kyau ya gani da idanunshi

-Ya bayyana haka ne a wata ziyara da ya kai a wata kotun majistire da ke a Ilorin inda kuma ya bukaci alkalin alkali na jihar da ya rubuto matsalolin da suke fuskanta

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya ce yana zagayen ziyara a wurare daban daban a fadin jihar don ya ga kalubalen da ke gabanshi.

Gwamna AbdulRazaq, ya bayyana cewa yana kai ziyarar ba zata a ma’aikatun gwamnati, don ya na bukatar ganin matsalolin da ke akwai da idanunshi ta yadda zai san hanyar magance su.

Da yake jawabi a ranar Talata 2 ga watan Yuli 2019, a lokacin da ya kai ziyara kotun majistire dake a Sango a birnin Ilorin, gwamna AbdulRazaq ya ce ya fara wannan zagaye ne ga ma’aikatun gwamnati don ya duba irin lalacewar da sukayi.

Ya bayyana cewa, lalacewar ta kai intaha kuma akwai bukatar a tsara kasafin kudi na shekaru don yin gyaran wajajen.

KARANTA WANNAN: Yanzu Yanzu: Tsohon ministan PDP da dan sa sun karbi katin zama 'yan APC

Ya ce: “Na zo na gane ma kaina. Tuni daman mun sani lalacewar ta kai intaha. Amman dai ya na da kyau da na zoi na gani da kaina.”

“Na gane ma kaina abubuwa da yawa kuma na gayamna alkalin alkalai (da mutanenshi) su rubuto matsalolinsu kuma su fadi abun da za mu iya yi wajen magance wannan matsaloli na lokaci mai tsawo.” A cewarshi

Gwamna Abdul Razaq ya ce zai tabbata an baiwa bangaren shari’a duk wata gudunmuwa da suke bukata ta yadda za su yi aikinsu a matsayin bangare mai zaman kanshi.

Alkalin alkalai na jihar, Mai shari’a Suleiman Kawu ya bayyana ma gwamnana cewa tun da dadewa ya rubuta rahoto akan irin lalacewar alamurra, musamman irin yadda gine ginensu suka lalace da kuma rashin dakunan kotu na zamani.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel