Sarkin Benin ya na nema a sasanta Oshiomhole da Obaseki

Sarkin Benin ya na nema a sasanta Oshiomhole da Obaseki

Kamar yadda mu ke samu labari a tsakiyar makon nan, majalisar Sarakuna da masu kasa na jihar Edo sun nemi sa-bakin manya a game da rikicin siyasar da ta kunno-kai a cikin jihar kwanan nan.

Shugaban wannan majalisa ta Sarakunan kasar Edo watau Mai martaba Oba na Benin, Omo B’Oba B’Edo ya mika wannan kokon-bara a lokacin da ya yi wata ganawar sirri da shugaban kasa Buhari.

Oba Omo B’Oba B’Edo Ewuare II ya fadawa shugaban kasa cewa rikicin da a ke yi tsakanin gwamna mai-ci da tsohon mai gidansa da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar yana matukar damunsu.

Oba na Benin ya ke cewa:

KU KARANTA: PDP: Ya kamata shugaban APC Oshiomhole ya mika kan sa gaban EFCC

“Ya Shugaban kasa, mu a matsayin mu na Sarakunan gargajiya na jihar Edo, rigimar shugaban APC na kasa, Kwamred Adams Oshiomhole, da kuma Mai girma gwamnan Edo Godwin Obaseki, da ‘yan majalisar dokokin jihar ya na ci mana tuwo a kwarya.”

Sarkin ya kuma nuna cewa wannan rikici zai iya cin jihar Edo idan har a ka yi sake abin ya yi kamari. Wannan ya sa Mai martaba Oba Omo B’Oba B’Edo ya roki a yi maza a sulhunta manyan.

A zaman da a ka yi a Aso Villa Ranar 3 ga Watan Yuni, 2019, Sarkin ya cigaba da fadawa shugaba Muhammadu Buhari cewa “Idan har ba a shawo kan wannan rikici tun da wuri ba, jihar na iya samun kanta cikin matsala a nan gaba.”

“A madadin daukacin al’ummar jihar Edo, mu na rokon alfarma wajen shugaban kasa da ya yi amfani da ofishinsa ya sa baki, a tsaida wannan rigima.” Inji Mai martaban.

Ba mu samu labarin martanin da shugaba Buhari ya bada a taron ba. Amma yanzu a na ta faman rikici a jihar Edo tsakanin manyan APC a daidai lokacin da ya kamata shiryawa zaben gwamna na badi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel