Majalisa: Ba mu yi na’am da wadanda a ka ba mukamai ba – 'Ya 'yan PDP

Majalisa: Ba mu yi na’am da wadanda a ka ba mukamai ba – 'Ya 'yan PDP

Jam’iyyar PDP ta nuna cewa ba ta amince da wadanda a ka ba jagorancin marasa rinjaye a majalisar wakilai ba. Hakan na zuwa ne bayan Femi Gbajabiamila ya yi watsi da takardar PDP.

Shugaban PDP na kasa, Uche Secondus, ya aikawa Gbajabiamilla takarda inda ya nemi a ba Kinsgley China, Chukwuka Oneyema, Yakubu Barde da Moraino Ajibola mukaman da a ka warewa ‘yan adawa.

Sai dai sabon kakakin majalisar wakilan, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya yi watsi da wannan roko na PDP inda ya nada Ndudi Elumelu, Toby Okechukwu, Gideon Goni da kuma Adesegun Adekola a kan mukaman.

Majalisar ta yi amfani ne da dokar ta wanda ta ce ‘ya ‘yan jam’iyya a majalisa ne za su zauna sun tsaida wadanda su ke so ba matsayi. Wannan abu dai ya jawo rikicin gaske tsakanin ‘yan majalisar hamayya.

KU KARANTA: PDP ta yi kaca-kaca da Shugaban APC ta ce ya sallama kan sa a gaban EFCC

Kingsley Chinda ya yi kokarin kawo hargitsi a majalisar bayan da ya ji an kira sunayen wasu a matsayin shugabannin marasa rinjaye inda daga baya ya fadawa ‘yan jarida cewa APC ce ke amfani da wasu ‘Yan PDP.

A na su bangaren Ndudi Elumelu da sauran wadanda a ka nada sun amince da wannan mukami da nauyi a ka daura a kan su. Elumelu ya ce an bi tsarin mulki da ka’idojin majalisa wajen wannan nadi da a ka yi.

A 2015 an samu irin wannan inda shugaban majalisar dattawa ya hau kujerar na-ki, ya yi watsi da takardar da jam'iyyar sa ta APC a lokacin ta aiko masa, ya nada wasu daban a kan mukami.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel