Oshiomhole ya je gaban EFCC ya wanke kan sa, ya kyale mu - Ologbondiyan

Oshiomhole ya je gaban EFCC ya wanke kan sa, ya kyale mu - Ologbondiyan

Labari ya zo gare mu cewa jam’iyyar adawa ta PDP ta yi kira ga shugaban APC na kasa, Kwamred Adams Oshiomhole, da ya ji da tarin zargin da ke gabansa a maimakon yunkurin sukar jam’iyyar.

Babbar jam’iyyar hamayyar kasar ta fitar da jawabi inda ta shawarci shugaban APC da ya mika kansa zuwa ga hukumar EFCC da kuma DSS a kan zargin satar dukiyar al’umma da a ke masa.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP watau Kola Ologbondiyan, shi ya fitar da wannan jawabi a Ranar Laraba, 3 ga Watan Yuni, 2019. Ologbondiyan ya ce hukuma na binciken tsohon gwamnan.

Kola Ologbondiyan ya ke cewa a na zargin Oshiomhole da tafka barna iri-iri a lokacin yana rike da jihar Edo har kuma zuwa lokacin da ya dare kujerar shugabancin jam’iyyar APC mai mulki.

KKU KARANTA: Kujerar Gwamnan Edo ta na rawa kan rikicinsa da Oshiomhole

Mai magana da yawun jam’iyyar ya ce a dalilin binciken da a ke yi wa shugaban na APC ne ya tsere daga kasar a bara da hukumar DSS ta taso shi gaba da zargin wawurar dukiyar Bayin Allah.

Bayan haka Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa Oshiomhole da bakinsa ya tabbatarwa Duniya cewa bata-gari ne ke cikin APC a lokacin da ya ce ana yafewa duk wanda ya shiga tafiyar APC.

PDP ta ce: "Akwai abubuwan da ya kamata Oshiomhole ya damu da su, ganin yadda ya ke ta fama da tarka-tarkar siyasa a jiharsa inda ya ke kokarin yi wa Magajinsa da ya kakaba a kan mulki karfa-karfa.”

PDP ta kuma ce: “Ya kamata Oshiomhole ya maida hankali kan rikicin da ya barkowa jam’iyyarsa da kuma fadar shugaban kasa inda a ke faman rikici game da mukaman gwamnati bayan APC ta murde zaben 2019.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel