Babu cacar-baki tsakani na da EFCC illa ni a ke yi wa sharri inji Saraki

Babu cacar-baki tsakani na da EFCC illa ni a ke yi wa sharri inji Saraki

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya maida martani game da wasu kalamai da ya fito kwanaki daga bakin hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin kasa zagon-kasa.

Bukola Saraki ya fadawa hukumar cewa ba ya fada da su kamar yadda su ke fadawa Duniya. Saraki ya bayyana wannan ne ta bakin Mai magana da yawunsa, Mista Yusuph Olaniyonu, a cikin Birinin Abuja.

“A gaskiya ma, Saraki ne ya ke shan soke a kafafen yada labarai iri-iri daga ofisoshin EFCC. Hukumar EFCC ta saba ba wasu ‘yan jarida takardu na shari’ar da a ka yi a kotu tsakanin ta da Saraki domin a wallafa.”

Olaniyonu ya ke cewa:

“Kai mu na mamakin yadda takardar da Bukola Saraki ya rubutawa hukuma a farkon Watan Mayu ta shiga hannun ‘yan jarida a Ranar Lahadin da ta gabata.”

KU KARANTA: Idan Saraki ya na da gaskiya ka daina jin tsoron Magu – EFCC

“Da a ce mu na da niyyar fito da wasikar da a ka rubuta, ba za mu jira sai bayan makonni 7 ba. Saraki ya fahimci doka kuma babu abin da ya ke jin tsoro. Bai da laifi a zargin da a ke yi masa.” Inji mai magana da yawun na sa.

“Ya kamata mu sake jaddadawa jama’a cewa Saraki bai da nufin hana EFCC ko wata hukuma bincikensa. Maganar da EFCC ta ke yi na cewa za a binciki ofishin shugaban majalisa daga 2015 zuwa 2019, duk wani zance ne.”

A game da binciken da a ke yi wa Saraki a lokacin ya na gwamnan Kwara daga 2003 zuwa 2011 kuwa, Hadimin na sa ya ke cewa ba yau a ka fara bankado wadannan zargi ba domin babu kotun da ba a shiga ba.

A kwanaki an binciki Saraki a kotun CCT mai bibiyar kadarori, har zuwa kotun daukaka kara, wanda a karshe a ka tike a gaban kotun koli inda shugaban majalisar ya samu nasara a kan hukuma.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel