Kotu ta bada umarnin a kamo shugaban hukumar Kwallon kafa ta kasa

Kotu ta bada umarnin a kamo shugaban hukumar Kwallon kafa ta kasa

- Wata babban kotu da ke Abuja ta bayar da umarnin kamo shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa, Amaju Pinick

- Mai shari’a Ijeoma Ojukwu, ta ce ta yanke wannan hukuncin ne duba ga cewa Shugaban hukumar kwallo kafar ya ki bayyana a kotu duk da cewar ta shi umarnin yin hakan

- Ana tuhumar Pinick da lakume kudi har Dala Miliyan 8.4 a lokacin gasar kwallo kafa na cin kofin duniya a Brazil a shekarar 2014

Rahotanni sun kawo cewa wata babban kotu da ke Abuja ta bayar da umarnin kamo shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa, Amaju Pinick.

Alkalin kotun, mai shari’a Ijeoma Ojukwu, ta ce ta yanke wannan hukuncin ne duba ga cewa Shugaban hukumar kwallo kafar ya ki bayyana a kotu duk da cewar ta shi umarnin yin hakan.

Ijeoma Ojukwu, ta ce dole a taso keyar sa ya bayyana a kotu a zama na gaba, wacce za a yi a ranar 28 ga watan Satumba.

Ana tuhumar Pinick da lakume kudi har Dala Miliyan 8.4 a lokacin gasar kwallo kafa na cin kofin duniya a Brazil a shekarar 2014.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda, sun kashe mutum 4 sannan suka tsere da bindigogi

Har ila yau kuma ana tuhumar su da shirya gasar karya domin yin sama da fadi da wasu kudade da sunan wai sun yi amfani da su a wajen shirya wadannan wasanni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel