AFCON: Kadan ya rage 'yan wasan Najeirya su yi bore saboda alawus

AFCON: Kadan ya rage 'yan wasan Najeirya su yi bore saboda alawus

Rahotanni sun nuna cewa kiris ya rage yan wasan kwallon kafa na Najeriya su yi bore akan alawus dinsu. Hakan na zuwa ne yayinda suke dab da tunkarar kasar Madagascar a wasan rukunin karshe.

Hukumar kwallon kafar Najeriya (NFF), ta biya yan wasan dukkanin kudaden da suke bi har zuwa ranar 30 ga watan Yuni, 2019.

Irin haka dai ta so faruwa a lokacin da suke shirin tunkarar kasar Guinea a ranar Laraba, lamarin da ya yi sanadiyyar da daya daga cikin 'yan wasan na Najeriya kin halartar taron manema labarai da ake yi kafin fara wasa sannan kuma 'yan wasan sun je filin atisaye a ranar Talata gabanin wasan a makare.

Tsoron abin da ya afku kafin wasan Najeriya da Guinea ne dai ya sa Hukumar kwallon kafar Najeriya ta yi saurin zuba wa dukkanin 'yan wasan alawus dinsu a cikin asusunsu na bakuna, a ranar Juma'a.

KU KARANTA KUMA: Kuma dai: Jam’iyyar APC ta dakatar da wani zababben dan majalisa a Edo

A tattaro cewa tawagar 'yan wasan na Najeriya da ta kasance a sansani guda tun farko watan Yuni, ta sami alawus ne daga ranar 9 zuwa 30 ga watn Yuni ne kadai.

Mataimakin kaftin din kungiyar wasan na Najeriya, Ahmed Musa ya dage cewa a koyaushe hankalin 'yan wasan na kan abin da ya kai su duk da irin abubuwan da suke faruwa masu dauke hankali da kuma batun alawus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel