Gwamnatin Najeriya ta fara aikin samar da ruga domin makiyaya a wasu jihohin Arewa

Gwamnatin Najeriya ta fara aikin samar da ruga domin makiyaya a wasu jihohin Arewa

-Gwamnatin tarayya ta fara gudanar da aikin samar da rugar makiyaya a jihohin arewa guda 11

-Jihohin da za zu amfana da wannan aikin sun hada da; Sokoto, Taraba, Kaduna, Nasarawa da wasu guda 7

Duk da ce-ce kuce da zancen samar da rugagen ya haifar daga bangaren jama’a, gwamnatin tarayya ta yi biris da duk wani surutu inda take shirin fara gudanar da aikin a jihohin Taraba, Adamawa, Filato, Kaduna da wasu jihohin guda 7.

Jaridar Satuday Punch ita ce ta tattaro mana wannan labari. Zancen da ya fito daga Abuja a ranar Juma’a na nuna cewa za’a fara aikin ne a jihohi 11 na Arewacin Najeriya cikinsu hadda: Sokoto, Nasarawa, Kogi, Katsina, Kebbi, Zamfara da Neja.

KU KARANTA:Ma’aikatan Kogi na cikin takaicin rashin biyan albashi

A wata takardar da wakilin Saturday Punch ya samu gani a Ma’aikatar Noma da Cigaban Karkara ta kasa, ta nuna cewa an riga da an kammala duk wani shirye-shirye na fara wannan aiki.

Haka zalika, wani babban jami’in ma’aikatar ya shaida mana cewa, gwamnati za ta cigaba da wannan shirin nata duk da surutai daga wurin jama’a musamman ‘yan kudancin kasar nan.

“ Jihohin da za su amfana da wannan aikin su ne: Sokoto, Adamawa, Kogi, Nasarawa, Kaduna, Katsina, Kebbi, Zamfara, Filato, Neja da Taraba. Jihohin guda 11 ne, gwamnonin wadannan jihohin za su zo ma’aikatar noma domin jin yadda wannan tsarin na ruga zai kasance.” Inji babban jami’in ma’aikatar wanda ya nemi a boye sunansa.

Ya cigaba da cewa: “ Wadannan sune jihohin da suka nuna sha’awarsu ga tsarin. Amma sai ga shi jama’a na ta zuzuta batun tamkar gwamnatin tarayya zata karbe filaye ne kawai a jihohin ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel