Yanzunnan: Ana artabu tsakanin Soji da yan Boko Haram a Yobe

Yanzunnan: Ana artabu tsakanin Soji da yan Boko Haram a Yobe

Rahoton Sahara Reporters na nuna cewa yanzu haka yan Boko Haram na artabu da jami'an soji a karamar hukumar Gujba dake jihar Yobe, Arewa maso gabashin Najeriya, majiyar tsaro ya bayyana.

Game da cewar majiya, yan Boko Haram sun kai harin ne misalin karfe 6 na yamma a garin Goneri.

Yace: "Yanzu haka yan Boko Haram na musayar wuta da jami'an soji a garin Goneri, karamar hukumar Guja a jihar Yobe. babu cikakken bayani yanzu."

Bayan gurmuzu na tsawon lokaci, Dakarun Soji na 120 Task Force Battalion da ke Goniri a jihar Yobe sunyi nasara kashe 'yan ta'adda masu yawa a wani harin kwanton bauna da suka kai musu misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Laraba.

Sojojin sun kafa tarko ne inda suka jira 'yan ta'addan suka matso kusa sannan suka yi musu luguden wuta a yayin da suka taho a motoccinsu masu dauke da bindigu guda bakwai.

Kakakin Rundunar Sojojin Najeriya, Kwanel Sagir Musa ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Alhamis inda ya ce 'yan ta'addan sun yi niyyar kai hari ne cikin motocci bakwai da babura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel