EFCC: ‘Dan damfara zai yi zaman gidan kurkuku a Jihar Kwara

EFCC: ‘Dan damfara zai yi zaman gidan kurkuku a Jihar Kwara

Mun samu labari cewa babban kotun jihar Kwara da ke zama a Garin Ilorin ta yankewa wani Matashi da ya kware a harkar damfarar jama’a mai suna Temitope Charles dauri a gidan yari.

Babban Alkali mai shari’a Mahmud Abdulgafar, ya yanke wannan hukunci bayan dogon zaman da kotu ta yi. Alkalin kotun ya samu wanda a ke zargi da duka laifuffuka 5 da a ke zargin sa da su.

Kotu ta yankewa Tope Charles daurin shekaru 7 ne a gidan yari a kan kowane laifin da a ka same shi da su. Hakan na nufin Matashin zai shafe shekaru 35 a gidan yari ba tare da damar biyan tara ba.

KU KARANTA: Kotu ta wanke Mahaifiyar Maryam Sanda daga zargin sata

Lauya AB Bakare wanda shi ne ke kare wanda a ke tuhuma, ya roki kotu ta yi masa rangwame. Barista Bakare ya roki Alkalin ya yi wa wanda a ke zargi afuwa domin bai taba yin wani laifi ba.

A wani bangaren, Lauyan da ke kara watau Barista Sesan Ola, ya nuna adawarsa ga bukatar wanda a ke tuhuma inda ya nemi Alkalin ya yanke masa hukunci gwargwadon laifin da ya aikata.

A cikin Watan Maris ne hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa su ka fara gurfanar da Charles a kotu da zargin damfarar jama’a da kuma zamba cikin aminci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel