ICPC: Alkalin kotu ya yi watsi da zargin da ke kan Maimuna Aliyu

ICPC: Alkalin kotu ya yi watsi da zargin da ke kan Maimuna Aliyu

A yau Laraba dinnan, 26 ga Watan Yuni, 2019, mu ka samu labari cewa kotun da ke shari’ar tsohuwar Darektar kamfanin nan na Aso Savings and Loans, Maimuna Aliyu, ya yi watsi da karar.

Wani babban kotun tarayya da ke zama a Jabi da ke cikin babban birinin tarayya Abuja ya yi fatali da karar ne bayan an dauki dogon lokaci a na shari’a tsakanin Aliyu da hukumar ICPC.

Hukumar ICPC mai yaki da sata a Najeriya ta na zargin tsohuwar Darektar ta Aso Savings & Loans da karkatar da wasu makudan kudi har Naira miliyan 57 a lokacin da ta ke aiki da kamfanin.

A shekarar 2017 ne shugaban kasa Buhari ya nada Maimuna Aliyu cikin manyan hukumar ICPC wanda hakan ya sa a ka bankado zargin da ke wuyar ta har a ka kai ga shiga kotu domin shari’a.

KU KARANTA: An tsinci wasu Masoya a mace cikin jini tsamo-tsamo a Legas

A karshe Alkali mai shari’a M. A ya yi wurgi da duka zargin da ake yi wa Hajiya Aliyu. Alkalin ya yanke wannan hukunci ne a wani zama da ya yi yau Laraba a kotun na sa da ke Abuja.

Lauyoyin wannan Baiwar Allah sun aika mata takarda da sa hannun Barista JK Gadzama wanda ke nuna cewa sun yi nasara a kotu. Takardar ta na nuna cewa Lauyoyin ta sun samu galaba.

Babban Lauya JK Gadzama ya ke fadawa wanda a ke tuhumar cewa kotu ta wanke ta kal, sannan ya gode mata na aiki da ta tayi da Lauyoyinsa, bayan taya ta murnar tabbatar da gaskiyar ta.

Idan ba ku manta ba, Hajiya Maimuna Aliyu, ita ce Mahaifiyar Maryam Sanda wanda a ke zargi da laifin kashe Mijin ta Marigayi Bilyaminu Bello. Wannan ya faru ne wani lokaci a karshen 2017.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel