'Yan ta'adda sun tashi kauyen Rafin Kada, sun kashe mutane da dama

'Yan ta'adda sun tashi kauyen Rafin Kada, sun kashe mutane da dama

Wasu kungiyar 'yan binida sun kai hari garin Rafin Kada da ke jihar Taraba inda suka kashe mutane da dama.

Sun kai harin ne a garin na Rafin Kada da ke hanyar Takum zuwa Wukari a safiyar ranar Talata.

Daily Trust ruwaito cewa 'yan bindigar sun shigo garin na Rafin Kada ne daga jihar Benuwe inda suka kone gidaje masu yawa kuma suka kashe mutane da dama.

'Yan bindigan kuma kaiwa motar shugaban karamar hukumar Wukari hari da wata mota dauke da sojoji a hanyarsu ta zuwa garin Rafin Kada domin amsa kirar neman dauki da aka yi musu.

DUBA WANNAN: Kishin-kishin: An bayyana lokacin da Buhari zai nada sabbin ministoci

An kuma ruwaito cewa 'yan bindigan sun yi wa wasu matasan garin Rafin Kada kwanton bauna inda suka kashe guda biyu cikinsu a yayin da suka yi yunkurin bin sahun 'yan bindigan domin daukan fansa.

Rafin Kada shine garin 'yan kabilar Jukun na uku da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kaiwa hari tare da kashe mutane cikin mako daya.

Shugaban karamar hukumar Wukari, Mr Adi Daniel ya shaidawa majiyar Legit.ng a hirar tarho cewa 'yan bindiga masu yawa sun kai hari a Rafin dadi a safiyar yau Talata.

Ya ce maharan sun kashe wasu mutane tare da kone gidaje 32.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Taraba, DSP Davida Misal ya tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga daga Benue sun shiga wata garin 'yan kabilar Jukun da ke kusa da Wukari inda suka kashe mutum daya kuma suka kone mutane da yawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel