Laifin sata: Darektocin hukumar REA za su yi zaman gidan yari

Laifin sata: Darektocin hukumar REA za su yi zaman gidan yari

Wani babban kotun tarayya da ke Abuja ya samu tsofaffin Darektocin hukumar da ke da alhakin hada wutar lantarki a karkara watau REA da laifin bacewar wasu kudi sama da Naira Biliyan 5.

Alkalin wannan kotu da ke zama a Abuja ya samu wadannan Darektoci da hannu wajen wawurar Biliyan 5.2 daga asusun hukumar REA, don haka a ka yankewa kowanen su hukuncin dauri.

Mai shari’a Adebukola Banjoko, shi ne ya yanke wannan hukunci a Ranar Juma’a, 21 ga Watan Yuni, 2019. Wanda aka samu da laifi sun hada da tsohon shugaban REA na kasa Samuel Ibi Gekpe.

Sauran Darektocin da a ka samu da laifi su ne: Injiniya Simon Kirdi Nanle, Abdusamad Garba Jahun, da wani babban jami’in bangaren shari’a na hukumar tarayyar mai suna Kayode Oyedeji.

KU KARANTA: Gwamnan Borno ya dakatar da wasu ma’aikata a wurin aiki

Mai shari’a Adebukola Banjoko ya samu wani Ma’ajin kudi na hukumar a lokacin da wannan abu ya faru watau Kayode Orekoya da hannu dumu-dumu bayan hukumar EFCC ta shigar da kara.

Wadanda a ka samu da laifin za su yi shekara 3 zuwa 5 a kurkuku. An kuma bada damar wadanda a ka kama da laifin su biya tara na N500, 000 zuwa Naira miliyan 5 domin su fanshi kansu a kotu.

Daga cikin wadanda a ke tuhuma da laifi akwai wanda kotu ta wanke bayan gudanar da shari’a. An samu wadannan jami’ai ne da laifin bada kwangila na bogi daga cikin kasafin kudin 2008.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel