Yanzu Yanzu: Abubuwan da muke sa ran Buhari zai duba wajen zabar ministoci - APC

Yanzu Yanzu: Abubuwan da muke sa ran Buhari zai duba wajen zabar ministoci - APC

- Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Oyo ta bayyana wasu muhimman abubuwa da ya kamata Shugaban kasa Buhari ya dua wajen zabar ministocinsa

- APC a jihar ta hannun daraktan labaranta, Dr Azeez Olatunde, ta lissafa sanin makamar aiki da cancanta a matsayin abunda ya kamata Buhari ya duba wajen zabar ministocin mataki na gaba

- Olatunde yace duba ga dumbin aikin da ke gaban gwamnatin APC a matakin tarayya a yanzu haka babu lokacin batawa

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Oyo ta lissafa manyan abubuwan da ya kamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya duba wajen zabar sabbin ministoci.

Da farko dai tace kamata yayi Buhari ya duba sanin makamar aiki sannan kuma abu na biyu ya duba cancanta wajen zabar ministocin mataki na gaba.

Jam’iyyar, wacce tayi Magana ta hannun daraktan labaranta, Dr Azeez Olatunde, tace babu gurbi ga ministocin da za su fara koyon aiki duba ga dumbin aikin da ke gaban gwamnatin APC a matakin tarayya a yanzu haka.

Olatunde yayi bayanin cewa majalisar dokokin tarayya ta takwas ta mayar da kanta abokiyar adawa, don haka ta dunga mayar wa gwamnatin tarayya da hannun agogo baya a kokarinta na kawo chanji kamar yadda tayi alkawari wanda shine dalilin da yasa yan Najeriya suka zabi yan takarar APC a 2015.

KU KARANTA KUMA: Madalla: Jama’a sun koma gidajensu a kauyukan Zamfara guda 6

Ya kara da cewa lamarin rashin tsaro da ake ciki a yanzu na bukatar kulawar gaggawa kamar yadda take kalubalantar kokarin gwamnatin tarayya na son tabbatar da cewa kasar ta samar da abinci ga al’ummanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel