Nagogo, sabon kwamishinan 'yan sanda a Zamfara ya fadi silar rikicin jihar

Nagogo, sabon kwamishinan 'yan sanda a Zamfara ya fadi silar rikicin jihar

Sabon kwamishina 'yan sanda a jihar Zamfara, Usman Nagogo, ya alakanta rikicin 'yan bindiga da ke faruwa a jihar da 'kisa ba bisa ka'ida ba' da mambobin kungiyar 'Yansakai' ke yi a fadin jihar.

Nagogo ya bayyana hakan ne a wurin wani taro da ya yi da shugabannin kungiyar 'Yansakai' a garin Gusau ranar Alhamis.

Ya ce rikicin jihar Zamfara ya fara ne da matsalar satar shanu amma daga baya ya gawurta bayan mambobin kungiya 'Yansakai' sun fara kashe 'yan ta'addar da aka kama ba bisa ka'ida ba.

"Kun san na yi aiki a jihar nan a matsayin mataimakin kwamishinan 'yan sanda a wasu shekaru da suka wuce.

"Na samu damar jagorantar kwamitin jami'in tsaro na tabbatar da zaman lafiya da tsohuwar gwamnatin jihar Zamfara ta kafa a wancan lokacin, kuma na tattauna da wasu daga cikin 'yan bindigar a matakin tattauna wa domin kawo karshen rikici a jihar Zamfara.

"Mun samu gagarumar nasara a lokacin, saboda 'yan bindiga da 'yan bijilanti da dama sun ajiye makamansu.

DUBA WANNAN: An gano dalilin da yasa Buhari ya sauke Baru daga shugabancin NNPC

"Na kira ku nan ne yau a matsayinku na shugabnnin wadannan kungiyo domin na sanar da ku cewar gwamnatin jiha tare da hadin gwuiwar jami'an tsaro za ta dawo da wancan sulhu da aka fara domin dawo kawo rikici a Zamfara.

"Hakan na daga cikin kokarin kawo karshen rikicin har abada," a cewarsa.

Kwamishinan 'yan sandan ya bayyana cewar 'kisa ba bisa ka'ida' ba ne ya jawo kai hare-haren daukan fansa da suka yi sanadiyyar asarar rayukan jama'a da lalata dukiya mai dumbin yawa.

"Kamar yadda muka sani, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya matukar damu da halin rashin tsaro da jihar Zamfara ke ciki.

“Babban sufeton 'yan sanda na kasa (IGP), Muhammad Adamu, ya kawo ni jihar Zamfa ne domin kawo karshen rikicin da jihar ta dade tana fama da shi, a saboda haka ina bukatar hadin kan ku," a cewar Nagogo.

Kazalika, ya bukaci shugabannin kungiyoyin 'Yansakan' da su bawa gwamnatin jihar Zamfara hadin kai a kokarin da take yi na tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel